Home Back

“Atiku Na Shirya Wani Abu”: Jagoran Ƴan Adawa Ya Ziyarci Buhari a Daura

legit.ng 2024/7/5
  • Rahotanni na nuni da cewa Atiku Abubakar, Aminu Tambuwal da wasu jiga-jigan jam'iyyar PDP sun ziyarci Muhammadu Buhari
  • Kamar yadda faifan bidiyo daban-daban ya nuna, jagororin jam'iyyar adawar sun gana da tsohon shugaban kasar a gidansa na Daura
  • Wannan dai na zuwa ne kasa da mako guda bayan Atiku ya ziyarci Ibrahim Babangida da Abdulsalami Abubakar a jihar Neja

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Daura, Katsina - Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar PDP, Atiku Abubakar ya ziyarci tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari a gidansa da ke Daura.

Atiku yana tare da tsohon gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal a yayin ganawarsu da tsohon shugaban kasar a wani faifan bidiyo da wakilin jaridar Legit Hausa ya gani.

Atiku ya gana da Buhari a Daura
Bidiyo: Atiku Abubakar ya ziyarci Muhammadu Buhari a gidansa da ke Daura. Hoto: @atiku, @MBuhari Asali: Facebook

Atiku, Tambuwal sun ziyarci Buhari

Daraktan kafofin sadarwar zamani na kungiyar Atiku The Light, Abdul-Aziz Na'ibi Abubakar ya wallafa bidiyon wannan ziyarar a shafinsa na X a yau Asabar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abdul-Aziz Na'ibi ya rubuta cewa:

A yau ne mai girma Atiku Abubakar ya kai ziyarar ban girma ga tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari a garin Daura.
"Atiku yana shirya wani babban al'amari."

Kalli bidiyon a kasa:

A wani kuma faifan bidiyon da muka gani a shafin @sir_balemoh na X, ya nuna cewa:

"Atiku ya isa gidan Muhammadu Buhari na Daura tare da Tambuwal, Dr. Mustapha Inuwa da sauran masu ruwa da tsaki na jam'iyyar PDP na shiyyar Arewa maso Yamma"

Kalliu bidiyon a kasa:

Wannan ziyarar dai na zuwa ne kasa da mako guda bayan Atiku Abubakar ya ziyarci Ibrahim Babangida da Abdulsalami Abubakar a jihar Neja, in ji rahoton The Cable.

Mun ruwaito Atiku Abubakar ya ce ya ziyarci tsofaffin shugabannin kasar na mulkin soja a gidajensu domin yi musu 'Barka da Sallah'.

Asali: Legit.ng

People are also reading