Home Back

Arsenal za ta kashe maƙudan kuɗi kan Luiz, Xavi na son kulob a Premier

bbc.com 2024/10/5
Douglas Luiz

Asalin hoton, Getty Images

Everton na tattaunawa don siyan Armando Broja daga Chelsea, Wolves sun amince da daukar Rodrigo Gomes daga Braga, Arsenal na neman Douglas Luiz.

Everton na tattaunawa don siyan Armando Broja daga Chelsea, Wolves sun amince da daukar Rodrigo Gomes daga Braga, Arsenal ta bayyana farashin Douglas Luiz.

Everton na tattaunawa don sayen dan wasan gaba na Albania Armando Broja, mai shekara 22, daga Chelsea a kan fan miliyan 30. (Ben Jacobs)

Wolves ta amince da cinikin dan wasan Portugal Rodrigo Gomes mai shekara 20 daga Braga. (Athletic)

An shaida wa Arsenal cewa za ta kashe fam miliyan 50 don siyan dan wasan tsakiyar Brazil Douglas Luiz mai shekara 26 daga Aston Villa. (Mirror)

Dan wasan tsakiya na Ingila Phil Foden, mai shekara 24, na shirin zama dan wasan Birtaniya mafi karbar albashi a tarihi, inda Manchester City ke shirin kara albashinsa zuwa £375,000 a mako. (Sun)

Arsenal da Manchester United sun ci gaba da zawarcin dan wasan Bologna dan kasar Holland Joshua Zirkzee, mai shekara 23, wanda AC Milan ke nema. (Sky Sports)

Bayern Munich ta gabatar da tayin farko, na kusan fan miliyan 30 kan dan wasan Fulham dan kasar Portugal Joao Palhinha, mai shekara 28. (Mail)

Tsohon golan Arsenal Jens Lehmann ya ce ba shi da tabbacin ko kociyan kungiyar na yanzu Mikel Arteta ne ya dace ya jagoranci kungiyar. (Telegraph)

Mamallakin kulob din Wrexham Rob McElhenney, ya ce bai yanke kauna ba, kan aniyarsa ta daukar tsohon dan wasan Wales da Real Madrid Gareth Bale, mai shekara 34, (Mirror)

Kulob din na Wales, yana kuma tattaunawa da golan Ingila Arthur Okonkwo, mai shekara 22, kan yarjejeniyar dindindin bayan Arsenal ta sako shi. (Talksport)

Kungiyar Al-Nassr ta Saudiyya na tattaunawa da golan Poland Wojciech Szczesny mai shekaru 34 don daukarsa daga Juventus. (Fabrizio Romano)

Newcastle na son dauko wani dan wasan gaba a wannan bazarar. (Football Insider)

Tsohon kocin Barcelona Xavi zai so ya jagoranci wani kulob da ke buga gasar Premier. (Sport Spanish)

People are also reading