Home Back

Muna Jaddada Kiran A Tsame Masarautunmu Daga Rikicin Siyasa

leadership.ng 2024/10/4
siyasa

Hankulan al’umma sun karkata a kan abubuwan da suke faruwa ko suke shirin aukuwa ga manyan sarakunanmu musamman na Arewa, yayin da a makon jiya, wasu rahotanni suka bayyana cewa Gwamnatin Jihar Sakkwato na shirin warware rawanin Mai Alfarma Sarkin Musulmi, Alhaji Sa’ad Abubakar II. Duk da cewa gwamnatin jihar ta fito fili ta musanta lamarin, amma kuma Majalisar Dokokin Jihar tana aiki a kan wani kudiri da ya rage wa sarkin ikon nada hakimai kai-tsaye ba tare da amincewar gwamna ba.

Ba a kammala jimamin wannan ba da na rikicin sarautar Kano, kwatsam a farkon makon nan kuma sai ga Gwamnan Katsina ya aike wa Mai Martaba Sarkin Katsina wata takardar neman bayani a kan rashin halartar wasu hakimai hawan sallah babba da aka yi kwanan baya. Saboda yadda wasu ke ganin laifin ya yi kankanta sosai a ce sarki mai daraja ta daya an tuhume shi kan wani abin da bai ta-ka-kara-ya karya ba wanda ko wani mai karamar sarauta zai iya warwarewa a fada, tabbas ya kara fitowa fili cewa abubuwan da gwamnonin ke yi wa masarautun, da walakin goro a miya. Sannan akwai kishin-kishin daga wasu jihohin ma cewa dangantaka ta riga ta yi tsami a tsakanin gwamnoni da manyan sarakunansu illa dai kowa yana jiran kilu ne ta jawo bau!

Shin me yake son faruwa ne da sarakunanmu masu martaba da suka zama cibiyoyinmu na asali shekaru aru-aru? Domin rabe tsaki da tsakuwa, mun sake kawo muku ra’ayinmu da muka wallafa a jaridarmu da ta fito ranar 7 ga Yuni, 2024.

A wani al’amari mai cike da takaici da kusan kowa ya sani, makircin siyasa a Jihar Kano ya sake jefa babbar masarautar jihar cikin wani yanayi wanda ba ita kadai abin ya taba ba har da ma yankin arewa.

Maido da Sanusi Lamido Sanusi a matsayin Sarkin Kano da Gwamna Abba Yusuf ya yi, tare da sauke wasu sarakuna biyar da gwamnatin da ta gabata ta nada, ya zama abin da al’umma ke ta tofa albarkacin bakinsu a kai game da halin da sarakunan gargajiya suka tsinci kansu a ciki yayin da suka shiga tsaka mai wuya a tsakiyar bangarancin siyasa.

Wannan labari mara dadi ba lamari ne da ya sha bamban ba; alama ce ta wani yanayi mai tayar da hankali da ya addabi jihohi daban-daban a fadin kasar nan.

Idan za mu iya tunawa, tsohon Gwamnan Jihar Kogi Yahaya Bello ya tsige wani basaraken gargajiya mai daraja ta daya, Ohimege Igu, na Koton-Nkarfe, Alhaji Abdulrazak Isa Koto.

Za mu kuma tuna cewa a shekarar 2022, sa’o’i 24 bayan hawansa mulki a matsayin Gwamnan Jihar Osun, Sanata Ademola Adeleke ya sauke wasu sarakunan gargajiya uku da magajinsa, Adegboyega Oyetola ya nada.

Tun daga Kogi zuwa Osun, da kuma Kano, mun ga yadda sarakunan gargajiya ke rungume hannu suna kallo ana korar su bisa son zuciya na gwamnatocin da ke hawa karagar mulki, galibi a matsayin ramuwar gayya kan abin da suka yi na mubaya’a, ko kuma a matsayin hanyar da za a tabbatar da kara karfin mulki.
A ra’ayin wannan jaridar, wannan wasan siyasa mai ban mamaki da ake yi wa cibiyoyin gargajiya ba wai kawai yana zubar da kimarsu ba ne har ma yana lalata tushen al’adun kasar nan da aka gada iyaye da kakanni ne.

Ana son masarautun gargajiya su kasance masu kula da dimbin tarihi da al’adun Nijeriya, wadanda ke tattare da gyara dabi’u, al’adu, da hikimomi wadanda ake gadar wa ‘yan baya.
Wadannan cibiyoyi sun kasance ababen girmamawa ba kawai a cikin al’ummominsu ba har ma a duk fadin kasar nan.

To sai dai idan suka zama ‘yan amshin shata a wasannin siyasa na masu rike da madafun iko, kwarjininsu da ikonsu na matukar raguwa, kuma amanar da talakawan suka ba su tana shiga cikin hadari.
Dole ne mu kula tare da killace cibiyoyinmu na gargajiya daga rugujewa sakamakon siyasar bangaranci. Dole ne a yi tir da kakkausar murya kan yadda gwamnoni ke korar sarakunan gargajiya tare da mayar da su kan karaga bisa manufa ta siyasa.

Irin wadannan abubuwa ba wai kawai suna zubar da mutuncin wadannan cibiyoyi ba ne, har ma suna haifar da sabani da rashin zaman lafiya a tsakanin al’ummomin da suka dade suna dogaro da hikima da jagoranci na sarakunansu na gargajiya.

Duk da yake gaskiya ya kamata sarakunan gargajiya su nesanta kansu daga siyasar bangaranci, kuma su ci gaba da kasancewa iyayen kasa, kowa nasu ne, ya kamata aikinsu na masu kula da abubuwan da aka gada na gargajiya da samar da zaman lafiya a tsakanin al’ummominsu ya kasance mara zargi.

Kamata ya yi a bar su, su sauke nauyin da ke kansu ba tare da tsoron fushi ko tsangwama ba daga ‘yan siyasa.

Ya kamata a lura da cewa, akwai kwararan dalilai na tsige sarakunan gargajiya, kamar samunsu da hannu wajen aikata laifuka, rashin biyayya, ko munanan dabi’u da ke barazana ga rayuwar al’ummarsu.
A irin wadannan lokuta, dole ne a bi tsarin da ya dace, kuma matakin da za a dauka ya kamata ya dogara ne a kan kwararan hujjoji kuma a gudanar da shi ta hanyar tsarin doka, ba son rai na siyasa ba.

Al’amuran da suka faru a Sakkwato, inda gwamnan jihar ya tsige hakimai 15 kan karagar mulki bisa zargin rashin biyayya, satar filaye, da taimakon rashin tsaro da kuma dakatar da wani basaraken gargajiya a Jihar Oyo bisa zargin alaka da masu hakar ma’adinai ba bisa ka’ida ba, misali ne na matakan da suka dace da aka dauka domin tabbatar kare mutuncin masarautun gargajiya da kare muradun mutanen da suke yi wa hidima.

To sai dai kuma halin da ake ciki a Kano, inda ake ganin mayar da sarki daya da tsige wasu daga mukaminsa na siyasa ne kawai, ya sha bamban da abubuwan da ake ganin na ka’ida ne.

Irin haka kuma yana lalata kimar wadannan cibiyoyi kuma yana haifar da karin rarrabuwar kawuna da bacin rai a tsakanin al’ummomin da tuni suke kokawa da kalubalen rashin tsaro da tashe-tashen hankula na zamantakewar al’umma.

Lokaci ya yi da al’umma za su fahimci gagarumar gudunmawar da cibiyoyin gargajiya za su iya bayarwa wajen samar da hadin kai, da kiyaye al’adunmu, da magance matsalolin da suka addabi kasar nan.
Wadannan cibiyoyi, idan aka mutunta su da kuma ba su karfi, za su iya zama kawance mai karfi na yaki da rashin tsaro, wadanda za su zama ginshikan tattaunawa, warware rikice-rikice, da fadada ci gaban al’umma.

Domin samun nasarar wannan, dole ne mu sanya karin kariya ga masarautunmu a cikin kundin tsarin mulkin kasa.

Dole ne a samar da sahihan tsare-tsare na nadawa, tsara wa’adin mulki, da tsige sarakunan gargajiya, tare da kawar da kai daga son zuciyar ‘yan siyasa da tabbatar da cewa aikinsu ya kasance bisa maslahar al’ummarsu ba tsarin bangaranci ba.

Bugu da kari, dole ne mu karfafa cibiyoyin gargajiya su rungumi aikin da ya dace a matsayin masu kula da l’adunmu na gargajiya da samar da zaman lafiya tare da nesantar siyasar bangaranci.
Ana iya samun nasarar hakan ta hanyar tabbatar da dorewar ilimin al’umma, tattaunawa da habaka mutunta wadannan cibiyoyi masu daraja.

Yayin da muke kai-komo a cikin sarkakiyar yanayin siyasar kasarmu, ka da mu manta da dimbin kima da muhimmancin da masarautunmu na gargajiya suke da su.

Ta hanyar kiyaye mutuncinsu da kuma kare su daga mummunar tasirin siyasar bangaranci, za mu iya tabbatar da cewa wadannan cibiyoyin sun ci gaba da zama ginshikan samun kyakkyawan fata da kuma kwanciyar hankali ga zurriyyar da ake hayayyafa.

People are also reading