Home Back

Mahaifiyar Rarara Ta Rasa Ranta a Hannun 'Yan Bindiga? Gaskiya Ta Bayyana

legit.ng 2024/10/4
  • Jaruma Aisha Humairah ta karyata rade-radin cewa mahaifiyar Dauda KahutuRarara ta rasa ranta a hannun masu garkuwa
  • Humairah ta bayyana haka ne yayin karin haske kan abin ake yadawa inda ta shawarci mutane su yi watsi da labarin
  • Jarumar ta ba da tabbata cewa da zaran Allah ya kubutar da Mama za ta fito ta yi bayani kamar yadda ta saba

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - An yi ta yaɗa rade-radin cewa mahaifiyar Dauda Kahutu Rarara ta rasa ranta a hannun masu garkuwa a kafofin sadarwa.

Sai dai Aisha Humairah ta karyata jita-jitar inda ta ce Mama, wato mahaifiyar Rarara tana nan cikin koshin lafiya.

Aisha ta bayyana haka a yau bayan sallar Juma'a a faifan bidiyon TikTok inda ta yi godiya ga masu taya su addu'a.

Jarumar ta ce duk lokacin da aka sako Mama za ta sanar da al'umma kamar yadda take yi inda ta roki mutane su bar yada jita-jita.

Wannan na zuwa ne bayan wasu sun yi ta yaɗa rade-radin cewa mahaifiyar mawakin ta rasu a hannun ƴan bindiga.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Dattijuwar ta shafe mako guda kenan a hannun ƴan bindiga inda suka bukaci kudin fansa har N900m.

'Yan bindiga sun sace mahaifiyar Rarara

A wani labarin, kun ji cewa ƴan bindiga sun shiga garin Kahutu da ke ƙaramar hukumar Ɗanja a jihar Katsina, sun yi garkuwa da mahifiyar Dauda Kahutu Rarara.

Rahotannin da Legit Hausa ta samu da safiyar ranar Jumu'a sun nuna cewa maharan sun ɗauki mahaifiyar fitaccen mawakin siyasar jiya Alhamis da daddare.

Asali: Legit.ng

People are also reading