Mahaifiyar Rarara Ta Rasa Ranta a Hannun 'Yan Bindiga? Gaskiya Ta Bayyana
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - An yi ta yaɗa rade-radin cewa mahaifiyar Dauda Kahutu Rarara ta rasa ranta a hannun masu garkuwa a kafofin sadarwa.
Sai dai Aisha Humairah ta karyata jita-jitar inda ta ce Mama, wato mahaifiyar Rarara tana nan cikin koshin lafiya.
Aisha ta bayyana haka a yau bayan sallar Juma'a a faifan bidiyon TikTok inda ta yi godiya ga masu taya su addu'a.
Jarumar ta ce duk lokacin da aka sako Mama za ta sanar da al'umma kamar yadda take yi inda ta roki mutane su bar yada jita-jita.
Wannan na zuwa ne bayan wasu sun yi ta yaɗa rade-radin cewa mahaifiyar mawakin ta rasu a hannun ƴan bindiga.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dattijuwar ta shafe mako guda kenan a hannun ƴan bindiga inda suka bukaci kudin fansa har N900m.
A wani labarin, kun ji cewa ƴan bindiga sun shiga garin Kahutu da ke ƙaramar hukumar Ɗanja a jihar Katsina, sun yi garkuwa da mahifiyar Dauda Kahutu Rarara.
Rahotannin da Legit Hausa ta samu da safiyar ranar Jumu'a sun nuna cewa maharan sun ɗauki mahaifiyar fitaccen mawakin siyasar jiya Alhamis da daddare.
Asali: Legit.ng