Home Back

Matasan NYSC biyu sun shafe watanni 9 hannun ‘yan bindigar Zamfara, ba ranar kuɓutar da su

premiumtimesng.com 2024/9/27
ABUJA TA DAGULE: Bayan garkuwa da mutum 11 a Dutse-Alhaji, ‘Yan bindiga sun yi garkuwa da wasu mutum 23 a Bwari

Biyu daga cikin matasan NYSC takwas ɗin da ‘yan bindiga suka kama, kan hanyar su ta zuwa aikin bautar ƙasa Jihar Sokoto, har yau su na cikin dajin Zamfara tsare a hannun ‘yan bindiga.

An kama su an yi garkuwa da su tun cikin watan Agusta, 2023 yayin da suka amsa kiran Gwamnatin Tarayya zuwa aikin bautar ƙasa na NYSC, a Jihar Sokoto.

Jama’a da dama tare da ƙungiyoyin kare haƙƙi na ci gaba da yin Allah wadai dangane da yadda aka ƙyale matasan biyu a hannun masu garkuwa da mutane, tsawon watanni 9 kenan.

Ana ci gaba da yin kira ga Gwamnatin Tarayya ta ɗauki duk wani matakin da ya dace domin kuɓutar da su.

Cikin Disamba NYSC ta ce ta samu karɓo biyu daga cikin waɗanda tsare ɗin, bayan sun shafe kwanaki 106 a hannun ‘yan bindiga.

Wasu mutane da ke da masaniyar yadda aka kuɓutar da 6 daga su, aka rage saura 2, sun bayyana cewa “akwai alamun NYSC ba su da ra’ayin sa hannu da sa baki wajen karɓo sauran mambobin na ta 2 daga hannun masu garkuwa da mutane a dajin Zamfara.

Sun zargi Gwamnatin Jihar Akwa Ibom da ƙin bada goyon baya kan kuɓutar da su.

Mafi yawan waɗanda aka yi garkuwa da su ɗin a lokacin, duk ‘yan asalin Jihar Akwa Ibom ne, ciki kuwa har da biyu ɗin da ke tsare har zuwa yanzu.