Home Back

Sabon Harajin Tsaron Yanar Gizo Bai Shafi Hada-hadar Kudi 16 Ba – CBN

leadership.ng 2024/5/20
Sabon Harajin Tsaron Yanar Gizo Bai Shafi Hada-hadar Kudi 16 Ba – CBN

Babban bankin Nijeriya (CBN), ya bai wa bankuna da cibiyoyin hada-hadar kudi umarnin fara cire harajin kashi 0.5 don tsaron yanar gizo.

CBN, ya ce harajin za a yi amfani da shi wajen yaki da masu datsar bayanan mutane ta yanar gizo kan harkar sha’anin banki.

Umarnin wanda ya bayyana a wata takardar da ke dauke da sa hannun daraktan sashen kula da tsarin biyan kudi, Chibuzo Efobi, da Haruna Mustafa, daraktan sashen tsare-tsare na kudi na CBN, ya bayyana cewa za ake cire sabon harajin ne a duk lokacin da mutane ya tura kudi.

Harajin zai fara aiki nan da makonni biyu daga ranar Litinin, kamar yadda CBN ya bayyana.

Amma babban bankin ya ce akwai akalla hada-hadar kudi 16 da sabon harajin bai shafa ba:

1. Bayar da bashi da kuma biyansa

2. Biyan albashi

3. Tura kudi daga wani asusu zuwa wani

4. Tura kudi daga wani banki zuwa wani bankin

5. Umarni daga wasu cibiyoyin kudi

6. Tsare-tsare a tsakanin bankuna

7. Tura kudi tsakanin bankuna da CBN

8. Tura kudi tsakanin reshen banki

9. Tantance caki da sauran hidimominsa

10. Takardun sanya kudi daga waje

11. Kudaden da ke da alaka da saka hannun jari a bankunan

12. Hada-hadar sanya kudi da adana su

13. Shirye-shiryen jin-kai na gwamnati

14. Hada-hadar kudi daga kungiyoyi masu zaman kansu

15. Hada-hadar kudi daga cibiyoyin ilimi

16. Tura kudi tsakanin asusun ajiyar banki

People are also reading