Home Back

Matsalolin Gidan Aure (3) Daure Fuska Da Rashin Nuna Damuwa Da Mace

leadership.ng 2024/6/29
aure

A yau shafin na mu zai ci gaba da kawo muku abubuwan dake kawo matsala a gidan aure da yadda za a magance su, inda muka tsaya a kan bayanin matsala ta biyu, kuma za mu dora.

Matsala ta uku:
Yana daure fuska: To idan ya daure fuska ke ya kike yi? To bai kamata ki daure taki fuskar ba lokacin da maigidanki ya daure fuska a lokacin ne ke ya kamata ki zama mai sakakkiyar fuska, ki yi masa wannan, ki yi masa wancan duk abin da kika san yana jin dadin sa shi ya kamata ki yi masa a wannana lokacin, idan kuma bai sauko ba za ki iya tambayarsa ko akwai wani abin da ya bata masa rai ko a gida ko a waje sai ki ba shi hakuri ki lallaba shi, ki sa shi ya yi wanka gajiya ta sauka ya ci abinci ki yi masa tausa za ki ga ya sauko. Sannan ki tambayi kanki wadannan tambayoyin don kara samun mafita.
A wane hali ya fita daga gidan? Ya kamata ki kasance mai farantawa maigida rai kafin ya fita ki shirya shi kin bashi abinci yaki karki barshi ya fita da yunwa, sannan ida zai fita ki raka shi har inda ya kamata kina mai masa addu’a tare da fatan alkhairi da nasara da sa’a a fitarsa.
Yaya yanayin Aikinsa yake? Wane yanayin aiikisa akwai wahala akwai gajiya za ki ga idan ya gaji ransa ya baci, ya kamata idan ya dawo ki zama mai tarairaya sannan kuma wadda za ta sauke masa gajiya a duk halin da yake to za ki ga yana son ya dawo gida saboda akwai wadda za ta tarairaye shi.
Da suwa Yake harka idan ya fita? Wasu abokan harka suna iya bata wa mutum rai to ya kamata ki gane haka saboda ki san ta yadda za ki kwantar masa da hankali.
Ya yanayin samunsa yake? Wani idan ya fita bai samo ba za ki ga wani yana bacin rai ko kuma idan bashi da kudi to ya kamata idan maigida bashi da kudi ki zama mai rarrashinsa tare da kwantar masa da hankali “Haba maigida ya kamata ka kwantar da hankalinka shi kudi ai na Allah ne idan yau baka da shi sai ka ga gobe Allah ya baka ire- iren wadannan kalaman haka sai ki ga hankalinsa ya kwanta.

Matsala ta hudu:
Bai damu da ni ba:
Kin sauke masa nauyin da Allah ya dora miki nasa a matsayinsa na mijinki? Idan kika nuna damuwarki a kansa kika bashi kulawa komai nasa kina nuna damuwarki kana kan ‘yan uwansa abubuwansa na rayuwa aikinsa ne komai da kika samu idan kina nuna damuwarki a kai to shima za ki ga yana nuna damuwarsa a kanki. Hakazalika, ki duba wadannan abubuwan ki tambayi kanki.
Kina kula da abin da yake so da wanda ba ya so? Ya kamata kisan abin da maigidanki yake so da wanda baya so saboda ki kiyaye duk abin da kika san ba ya so sai ki barshi koda kuwa ke kina son abin nan sai ki hakura.
Kina jin damuwarsa a ranki? Ya kamata ki zama mai damuwa da mijinki idan yana gidane ko kuma ya fita, nuna kulawarki a gare shi shi zai sa ya san kin damu da shi.
Shin kina masa wasa? Ki kasance mai wasa da mijinki a lokacin da kika ga yana cikin farin ciki yana kuma bukatar yin wasan sai ki ga idan yana wani wajen ya tuna da wasanki sai dai a ga yana dariya.
Shin kina nuna masa kula da mahaifansa da danginsa? Ki rika kulawa da iyayansa kina kyautata musu yadda yakamata daidai gwargwadon iyawarki idan mace tana kula da iyayen maigida to zai rika ji da ita.
Kina yi masa addu’a? Ki kasance mai yi masa addu’a idan zai fita Allah ya kiyaye Allah ya tsare Allah ya kai ka lafiya abin da ka fita nema Allah ya baka tsautsayi da asara Allah ya kiyaye min kai ire-iren wadannan addu’o’in, sannan idan ya yi miki kyauta ki yi godiya tare da addu’ar Allah ya kara budi.

People are also reading