Home Back

An ɓarke da biki bayan gogarman ƴan ta’adda Dogo Gide ya yi ƙaura daga Daji zuwa ƙauyen Magami da zama

premiumtimesng.com 6 days ago
AREWA A HANNUN ‘YAN BINDIGA: Tattaki a Daular Dogo Giɗe da Ali Kachalla, riƙaƙƙun ‘yan ta’addar da ke yadda suka ga dama a Arewa,suka gagari gwamnati

Mazauna garin Magami dake jihar Zamfara sun barke da shagulgula da bukukuwa da murna bayan ƙasurgumin ɗan ta’adda ya yi hijira ya koma zama dindin a wannan gari.

Giɗe dai shine wanda ya kirsa sannan ya sace ɗaliban makaranta a Kuriga, jihar Kaduna.

Daga baya an yi ta yaɗa wa wai ya rasu bayan wani arangama da ya yi da sojoji.

Ya samu raunuka a jikinsa da hakan yasa aka riƙa yadawa wai ya rasu.

Bayanai na baya-bayan nan daga mazauna yankin sun nuna cewa Gide ya tsallake rijiya da baya daga harsashin da sojoji suka yi ɗirka masa, kuma yanzu ya yi hijira daga maboyarsa ta Babban Doka a dajin Madada.

“Dogo Gide ya koma garin Kizara da ke gabar gabashin Magami. Ya umurci manoma da su koma gonakinsu ba tare da fargabar sace su ba ko kuma ɓarnata dukiyoyinsu ba.” , wani mazaunin garin ya shaidawa PREMIUM TIMES.

A cikin wata sabuwar waka da aka yi masa, an yabe sa ta yadda ba a zato.

Mutanen magami na cike da farin ciki ganin damar da ya basu na su koma gona babu wanda zai hana su ayyukansu musamman a yanzu da damuna ya kankama a Najeriya musamman Arewa.

People are also reading