Home Back

DOKAR TA-ƁACI KAN ILMI A KANO: ‘Mun gaji ɗaliban firamare miliyan 4.7 masu zama a ƙasa a zamanin mulkin Ganduje’ – Gwamna Abba

premiumtimesng.com 2024/6/25
DOKAR TA-ƁACI KAN ILMI A KANO: ‘Mun gaji ɗaliban firamare miliyan 4.7 masu zama a ƙasa a zamanin mulkin Ganduje’ – Gwamna Abba

Gwamna Abba Yusuf na Jihar Kano ya bayyana cewa gwamnatin sa ta samu ɗaliban firamare aƙalla miliyan 4.7 da ke zama a ƙasa su na ɗaukar darussa a zamanin mulkin tsohon Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje a faɗin jihar.

Abba ya yi wannan furuci ne lokacin da ya ke ƙaddamar da Dokar Ta-ɓaci kan Harkokin Ilmi a Jihar Kano, ranar Asabar, a Buɗaɗɗen Ɗakin Taro na Gidan Gwamnatin Kano.

Ya ce gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da dokar ta-ɓaci kan harkokin ilmi, tare da cikakken goyon bayan Ƙungiyar Malaman Makarantu ta Ƙasa (NUT).

Gwamnan ya jaddada cewa rashin kayan aikin koyar da karatu sun ƙara kambama matsalolin fannin ilimi, “aka bar malamai da ɗalibai su na gaganiya da tsoffin kayan aiki kuma waɗanda ba su wadata ba.

“Mun samu ɗalibai sama da miliyan 4.7 masu zama dirshan a ƙasa, su na ɗaukar darussa a cikin ajujuwa. Saboda rashin tebura da kujeru. Kuma kusan makarantun firame kamar 400 kowace malami ɗaya tal take da shi, a lokacin da muka hau mulki. Kuma shi wannan malamin shi kaɗai ke koyar da kowane darasi.

“Maimakon gwamnatin da muka gada ta ƙara gina ajujuwa a makarantu kuma ta samar da malamai da tebura da kujeru, sai ta riƙa kamfatar filayen da ke cikin makarantun ta na sayarwa, ana gina shaguna da kantina a cikin makarantun. A wasu wuraren ma har ajujuwa an rushe domin a samu filayen da za a gina shagunan kasuwanci.

“Makarantun da ba za su iya sayarwa ba kuwa, sai suka riƙa yin kaca-kaca da su, tare da rufe su.”

Ya ke magana kan yara waɗanda ba su zuwa makaranta kuwa, Gwamna Abba ya ce gwamnatin sa ta yi alƙawarin ɗaukar ƙwararan matakai domin magance matsalar da ke hana yaran zuwa makaranta.

“Abin takaici, wannan jiha ta mai albarka na fama da yaran da ba su zuwa makaranta da adadin su ya kai 989,234.” Inji shi.

Cikin waɗanda ke wurin har da Jagoran Kwankwasiyya, Sanata Rabi’u Kwankwaso, tsohon Gwamnan Jihar Ribas, Donald Duke da sauran manyan baƙi.

People are also reading