Home Back

Zanga-Zanga Ta Barke a Hedktwar Jam'iyyar PDP Ta Kasa Da Ke Abuja

legit.ng 2024/5/18

FCT Abuja - Wasu gungun masu zanga-zanga sun mamaye babbar hedkwatar jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP) da ke birnin tarayya Abuja.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Masu zanga-zangar sun ayyana cikakken goyon bayansu ga muƙaddashin shugaban PDP na ƙasa, Umar Damagum da ministan birnin tarayya, Nyesom Wike.

Kamar yadda Channels tv ta ruwaito, masu zanga-zangar sun ɗaga allunan sanarwa masu ɗauke da rubutun da ke nuna goyon bayansu ga Wike da Damagum.

Sun bayyana cewa suna zargin wasu tsirarin mutane a cikin jam'iyyar PDP na ƙoƙarin haifar da rashin jituwa da rabuwar kawuna a tsakanin shugabannin jam'iyya.

Ku saurari ƙarin bayani...

Asali: Legit.ng

People are also reading