Home Back

Sarautar Kano: Lauyoyin Aminu Ado sun Sau Ladansu A Ci Gaba Da Shari'ar da Ake Yi

legit.ng 2 days ago
  • Lauyoyin da ke kare Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero sun janye daga shari'ar da ake yi kan wasu zarge-zarge
  • Lauyoyin sun nuna rashin jin dadinsu kan yadda kotun ke daukar matakai da ba su hango adalci a ciki ba
  • Hakan ya biyo bayan ci gaba da dambarwa kan rigimar sarautar da ake ciki tun a watan Mayun 2024 da ta gabata

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Yayin da ake ci gaba da dambarwa kan sarautar Kano, lauyoyin Aminu Ado sun tsame jikinsu.

Lauyoyin sun janye ne a gaban Babbar Kotun jihar kan rashin jin dadinsu game da matakin da kotun ta dauka.

Barista Abdul Mohammed ya ce akwai matsaloli tattare da matakan da kotun ke dauka wanda ke kunshe da rashin adalci, cewar Daily Trust.

Lauyan ya ce ya bukaci kotun ta dage ci gaba da sauraran shari'ar amma ta ki ba su dama wanda hakan ya sake nuna akwai rashin gaskiya.

Daga bisani, Mohammed ya janye daga ci gaba da kasancewa a matsayin lauyan Sarkin Kano na 15, Aminu Ado Bayero.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Har ila yau, Barista Sanusi Musa a madadin sauran lauyoyin shi ma ya janye daga kare Aminu Ado.

Masu korafi a gaban kotun sun hada da kwamishinan shari'a na jihar Kano da kakakin Majalisar jihar.

Sai kuma Majalisar jihar da kanta wanda lauyansu Ibrahim Isah Wangida ya shigar da korafi a ranar 27 ga watan Yulin 2024.

Masu korafin suna neman kotun ta dakatar da Aminu Ado da sauran sarakuna hudu da aka tsige ci gaba kiran kansu masu sarauta.

Sarakuna guda hudun sun hada da na garuruwan Bichi da Karaye da Gaya da kuma Rano.

Kotu ta dage sauraron shari'ar sarautar Kano

Kun ji cewa Babbar Kotun jihar Kano da ke sauraron shari'ar sarauta ta yi zama kan rigimar inda ta dauki mataki a wannan mako.

Kotun ta dage ci gaba sauraron shari'ar har zuwa ranar yau Alhamis 4 ga watan Yulin 2024 domin daukar matakin gaba.

Asali: Legit.ng

People are also reading