Home Back

Ƙudirin doka na ƙirƙiro ƙarin Jaha a Najeriya ya tsallake karatu na ɗaya a Majalissa

dalafmkano.com 4 days ago

Majalissar wakilai ta Ƙasa ta gabatar da wani ƙudirin doka dake buƙatar samar da ƙarin wata sabuwar jaha da za’a sa mata suna da JIHAR ETITI, a kudu maso yammacin Najeriya.

Ƙudirin dokar wanda Ɗan majalissa Amobi Godwin Ogah, ya gabatar da ƙarin wasu mambobin mutum huɗu suka mara masa baya, yanzu haka ya tsallake karatu na ɗaya.

Rahotanni sun bayyana cewa gabanin tabbatuwar ƙarin sabuwar jihar dai wajibi ne sai ƙudirin dokar ya samar da gyaran manyan sashi-sahi guda uku dake cikin kundin tsarin mulkin ƙasa da aka gyara a shekarar 1999.

Idan akayi gyaran kundin tsarin mulkin dai zai koma jihohi 37 mai-makon talatin da shida da ake da su a kundin tsarin mulkin har da Abuja.

People are also reading