Home Back

CBN Ya Musanta Rahoton Soke Lasisin Wasu Bankuna a Najeriya

legit.ng 2024/7/5
  • Bankin CBN ya musanta rahoton da ke yawo cewa yana shirin soke lasisin bankunan Fidelity, Polaris, Wema da kuma Unity
  • Muƙaddashiyar kakakin CBN, Hakama Sidi Ali, ta yi ƙarin haske kan takardar da ke yawo a wata sanarwa da ta fitar ranar Litinin, 10 ga watan Yuni
  • Ta bukaci kwastomi su kwantan da hankalinsu domin kuɗafen da suka ajiye a asusunsu na nan cikin aminci da tsaro

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Babban bankin Najeriya (CBN) ya karyata zargin da ake masa na cewa yana shirin soke lasisin aiki na bankunan Fidelity, Polaris, Wema, da Unity.

Babban bankin ya yi wannam bayanin ne yayin da mutane suka fara shiga damuwa kan makomar bankunan ƙasar nan biyo bayan soke lasisin Heritage.

Gwamnan CBN, Yemi Cardoso.
Bankin CBN ya musanta soke lasisin bankunan Fidelity, Polaris. Wema da Unity Hoto: @cenbank Asali: Facebook

Hakan na ƙunshe ne a wata sanarwa da Hakama Sidi Ali, mukaddashin daraktan sashen sadarwa na CBN ta fitar ranar Litinin, 10 ga watan Yuni, 2024.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ta tabbatarwa kwastomomi cewa duk kuɗin da suka ajiye a banki na nan cikin aminci kuma babu abin da zai taɓa su, The Nation ta tattaro.

Hakama Sidi ta kuma yi ƙarin haske kan wata sanarwa da CBN ya fitar tun a ranar 10 ga watan Janairu, 2024 wadda ta rushe majalisar gudanarwa a bankunan Keystone da Polaris.

Legit Hausa ta fahimci cewa a yanzu ana ta yaɗa wannan sanarwa da sunan CBN ya fitat da ita ne yau Litinin, 10 ga watan Yuni, wanda ko kaɗan ba haka bane.

Kakakin CBN ya bayyana cewa wannan sanarwa ba ta yanzu ba ce, tsohon mataki ne da babban bankin ya ɗauka watannin da suka shuɗe.

"Lamarin bankin Heritage na daban ne," in ji Hakama, inda ta ƙara da cewa rahoton da ke yawo cewa ana shirin sake soke lasisin wasu bankuna ba gaskiya ba ne.

Ta kuma yi kira ga kwastomomi musamman waɗanda suka ajiye kuɗaɗen su a bankin Heritage kada su damu ko fargabar rasa haƙƙoƙinsu domin za a tura masu kuɗinsu.

A wani rahoton kuma

Asali: Legit.ng

People are also reading