Home Back

Gwamnan Kano Ya Ceto Iyalin Sarki Ado Bayero da Ake Neman Tozartawa a Gidan Haya

legit.ng 2024/10/6
  • Gwamnatin jihar Kano ta kai dauki ga diyar marigayi Sarki Ado Bayero saboda bayyana fargabar za a kore ta,mahaifiyarta da jami'inta daga gidan haya da ta yi
  • Gimbiya Zainab Ado Bayero ta nemi taimakon ƴaƴanta, Sarkin Kano na 15 Aminu Ado Bayero da na Sarki na 16, Muhammadu Sanusi II su gaza kar a kore su
  • Amma a sakon da darakta janar kan yada labaran gwamna Abba Kabir Yusuf, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar, ya ce gwamna ya shiga lamarin domin bai kamata a barsu ba

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. Jihar Kano- Gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta gaggauta shiga tsakani domin hana masu gidan hayar da diyar marigayi Sarki Ado Bayero ke zaune korarta. Matakin na zuwa ne bayan gimbiya Zainab Ado Bayero ta yi kururuwa cewa za a kore su yau da misalin ƙarfe 3.00pm idan basu biya kudin haya ba.

Sanusi
Gwamnatin Kano ta shiga batun gidan hayar diyar marigayi Sarki Bayero Hoto: Sanusi Bature Dawakin Tofa Asali: Facebook

A sanarwar da darakta janar na gwamnan jihar Kano kan yada labarai, Sanusi Bature Dawakin Tofa ya fitar a shafinsa na facebook, ya ce gwamna ya shiga lamarin

Gwamna Abba ya biya kudin haya

Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya biya kudin hayar gimbiya Zainab Ado Bayero, inda ta ke zaune da mahaifiyarta a wani gida da ke Victoria Island a jihar Legas. Darakta janar ka yada labarai na gwamnan Kano, Sanusi Bature Dawakin Tofa ne ya biya kudin mintina 15 kafin a fitar da su daga gidan da karfin tsiya. Gimbiya Zainab ta bayyana godiya bisa yadda aka fitar da su kunya a lokacin da su ke cikin tsananin bukata, kamar yadda Daily Trust ta wallafa Ana zargin Zainab da mahaifiyarta sun shiga mugun hali ne saboda hana su gadonsu bayan rasuwar Sarki Bayero.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Diyar Sarki Bayero ta nemi taimako

A baya mun kawo labarin cewa 'yar marigayi Sarkin Kano, Dr. Ado Bayero ta nemi daukin Sarkin Kano na 16, Muhammadu Sanusi II da na yayanta, Sarki Aminu Ado Bayero. Kan koka ne kan fargabar shirin korarsu da inda su ke zaune gidan haya ke kokarin yi a jihar Legas saboda gaza biyan kudin da ake binsu.

Asali: Legit.ng

People are also reading