Home Back

El-Rufai: Dan Majalisa Ya Bayyana Yadda Tsohon Gwamna Ya Bar Kaduna Cikin Matsala

legit.ng 2024/7/3
  • Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya zama abin magana bayan majalisar dokokin jihar ta yi bincike a kan gwamnatinsa
  • Shugaban kwamitin binciken ya yi zargin cewa tsohon gwamnan ya bar kaso 60% na ayyukan da ba a kammala ba duk da an gama biyan kuɗaɗensu
  • Ya yi zargin cewa gwamnatin El-Rufai ta karɓo basussuka ba tare da yin wani abu da su ba sannan cike ta ke da cin hanci da rashawa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Wani ɗan majalisar dokokin jihar Kaduna, Henry Marah, ya yi zargin cewa gwamnatin Nasir Ahmad El-Rufai ta bar kusan kaso 60% na ayyukan da ba a kammala.

Ɗan majalisan shi ne shugaban kwamitin wucin gadi na majalisar dokokin jihar Kaduna dake binciken gwamnatin tsohon gwamna Nasir El-Rufai na tsawon shekaru takwas.

Dan majalisa ya zargi El-Rufai da cin hanci
Dan majalisa ya zargi El-Rufai da karbo bashi ba tare da yin aiki ba Hoto: Nasir El-Rufai Asali: Facebook

Wane zargi aka yi kan El-Rufai?

Ya bayyana cewa kaso 60% na ayyukan da gwamnatin ta bari, an kammala biyan kuɗadensu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Henry Marah ya bayyana hakan ne dai a lokacin da ake hira da shi a tashar Channels tv a shirinsu na 'Politics Today' a ranar Laraba.

"A lokacin da El-Rufai ya hau mulki a 2015, dukkanin bashin cikin gida da gwamnatin da ta shuɗe ta ciyo, ta biya shi. Ya zo ya tarar babu bashin ko sisin kwabo sannan an bar masa N3bn domin ya fara gwamnatinsa."
"Yanzu je ka duba ka gani a bayanan miƙa mulki na El-Rufai bashin nawa ya bari. Sannan kuɗaɗen da ya karɓi domin yin ayyukan, sama da kaso 60% na waɗannan ayyukan an yi watsi da su."
"Sai ya ɗauki jihar Kaduna kusan shekara 20 kafin ta kammala abin da ya bari. Saboda haka ina gaskiyar take a nan?"

- Henry Marah

El-Rufai ya karɓo bashi ba aiki

Ya yi zargin cewa an karɓo basussuka masu yawa domin gudanar da ayyuka amma ba a yi ayyukan ba kuma kuɗaɗen sun yi ɓatan dabo.

A cewar ɗan majalisar an karɓo kuɗaɗe ba tare da yin wani abu da su ba. Ya yi zargin cewa gwamnatin El-Rufai cike ta ke da cin hanci sannan ta wawushe asusun jihar.

Ɗan majalisar ya yi iƙirarin cewa wasu basussukan da gwamnatin El-Rufai ta karɓo ba majalisar ta amince da su ba, kuma an yi sa hannun jabu na wasu ƴan majalisar domin amincewa da basussukan.

Yaushe za a gayyaci El-Rufai

Ya ce duk waɗanda suka yi aiki a gwamnatin da ta shuɗe kuma sa hannunsu ya bayyana a takardun da suka dace, an gayyace su kuma sun bayyana a gaban kwamitin amma ba a gayyaci El-Rufai ba.

Sai dai, Henry Marah ya ce za a ba El-Rufai damar kare kansa. Ya ƙara da cewa an aike da rahoton kwamitin ga hukumomin yaƙi da cin hanci da rashawa domin ɗaukar matakin da ya dace.

El-Rufai ya magantu kan bincikensa

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya yi martani kan zargin karkatar da ake yiwa gwamnatinsa.

Tsohon ministan na babban birnin tarayya Abuja ya yi fatali da rahoton majalisar dokokin jihar kan binciken gwamnatinsa daga shekarar 2015 zuwa 2023

Asali: Legit.ng

People are also reading