Home Back

Sakon Sallah: Gwamna Nasir Ya Yi Kira Da Hadin Kai Don Gina Jihar Kebbi

leadership.ng 2024/5/11
Sakon Sallah: Gwamna Nasir Ya Yi Kira Da Hadin Kai Don Gina Jihar Kebbi

Gwamnan jihar Kebbi, Dakta Nasir Idris, ya bukaci jam’iyyun adawa da su hada kai da gwamnatinsa domin gina kyakkyawan shugabanci da bunkasa tattalin arzikin jihar.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a fadar gwamnati da ke Birnin Kebbi a sakonsa na fatan alheri ga al’ummar jihar bayan halartar Sallar Eid-el-Fitr a babban masallacin Sallar Idi a Birnin Kebbi.

“Yanzu da aka kammala zabe da siyasa, ina gayyatar al’ummar jihar na kowane bangare ba tare da la’akari na jam’iyya ba. Mu hada kai na gani ci gaban jihar mu domin kaiwa ga matakin ci gaban da ake so”.

“Mafi yawan jama’a sun zabe ni, ina gode musu da sauran su bisa goyon bayan da suka ba ni, da aminci da kuma hadin kai,” inji shi.

Ya tabbatar da cewa gwamnati za ta tabbatar da samar da ababen more rayuwa, tattalin arziki, noma, bunkasa ilimi da samar da ingantattun ayyukan kiwon lafiya ga al’umma.

“Babban asibitocin da ke Argungu, Yauri da Zuru, za a gyara su tare da samar da kayan aiki na zamani don yi wa mazauna yankin hidima da kuma gudanar da ayyukansu a matsayin cibiyoyin kiwon lafiya ba tare da sun kawo masara lafiya a babban birnin Jihar ba” in ji shi.

Ya taya al’ummar jihar Kebbi murnar kammala azumin watan Ramadan da kuma murnar bukukuwan karamar Sallah.

Gwamna Nasir

Dakta Nasir Idris ya bukace su da su ci gaba da gudanar da addu’o’i na musamman domin samun nasarar gwamnati, zaman lafiya, tsaro da ci gaban al’umma.

Gwamnan ya kara da bayyana gamsuwarsa game da dawowar tsaro a yankin Kebbi ta Kudu wanda hakan ya sa manoman za su koma gonakinsu domin gudanar aikin noman rani da damana.

A nasa jawabin, karamin ministan ilimi, Dakta Tanko Yusuf Sununu, wanda ya yi Sallar Idi tare da Gwamna Nasir Idris, ya bukaci ‘yan Nijeriya da su ci gaba da yi wa gwamnatin Bola Ahmed Tinubu addu’a domin samun nasara a matakin tarayya da jihohin kasar nan.

Dokta Sununu ya bayyana Gwamna Nasir Idris a matsayin shugaba mai iya gudanar da mulki kamar yadda irin ci gaban da aka samu tun hawan mulkinsa zuwa yanzu.

People are also reading