Home Back

Fargaba bayan faduwar jirgi marasa matuki a Nijar

dw.com 2024/5/16
Jami'an tsaro da sojojin kasashen waje da a jibge a Nijar a baya sun saba amfani da jirgi marasa matuki
Jami'an tsaro da sojojin kasashen waje da a jibge a Nijar a baya sun saba amfani da jirgi marasa matuki

Tun bayan da Jamhuriyar Nijar ta tsinci kanta cikin matsalar ta'adanci ne gwamnantin kasar ke daukan matakai don shawo kan lamarin tsaro  a fadin kasar ciki har da jihar Tahoua, inda sojoji ke amfani da jirage marasa matuka wajen yaki da ta'adanci musamman ma wajen tattara bayanan sirri ko kai wa 'yan bindiga hari ta sama. Sai dai kasancewar na'urar a daya daga cikin wuraren ya sa ta cin karo tare da fadowa wata unguwa ba tare da ya haddasa wata mumunar barna ba, kamar yadda mazauna unguwar da abin ya faru suka shaida wa DW.

Faduwar jirgi marasa matukin ya jefa mazauna garin Tahoua cikin damuwa inda suke kallon jiragen a matsayin wata barazana ga tsaro da rayuwarsu, kamar yadda. Malam Aliyu da ke zama daya daga cikin masu wannan fargaba ya bayyana. Mutane da dama na ganin cewar shawagin da jirage marasa matuka ke yi a sararin samaniya na zaman wata barazana ga al'umma. Sai dai Mounkaila Amadou, wani mai sharhi kan al'amuran tsaro ya ce babu wani abun shan kai da ke kawo makamancin wannan tunanin kasancewar a kowane aiki a kan samu kuskure .

Mounkaila Amadou ya kara da cewar wani abin alfahari ne ga al'ummar Nijar kasancewar jiragen marasa natuka na nuna cewar gwamnantin na sa ido sosai a kantsaron lafiyar al'umma.  Wannan dai ba shi ne karo na farko ba da ake samun hadarin makamantan wadannan jirage marasa matuka ba a Jamhuriyar Nijar, inda ko a yankin Agadez sojojin Amirka ke amfani da su, ana samun faduwarsu amman ba tare da jikkata kowa ba.

People are also reading