Home Back

Bashir El-Rufai ya shiga wa ubansa faɗa, ya caccaki gwamna Uba Sani da maƙarraban sa

premiumtimesng.com 2024/5/2
Bashir El-Rufai ya shiga wa ubansa faɗa, ya caccaki gwamna Uba Sani da maƙarraban sa

A wata sabuwar badaƙalar siyasa da ta kunno kai a jihar Kaduna, a yau Asabar, gwamnan jihar Uba Sani, ya tabbatar da hannun rigar da suka raba tsakanin sa da tsohon gwamnan Jihar, Nasir El-Rufai inda ya bayyana cewa tsohon gwamnan ya karankatako ɗinɓin basuka daga kasashen waje a lokacin da ya ke gwamnan jihar.

Gwamna El-Rufai ne gwamnan Kaduna daga 2015-2023, da bayan ya kammala wa’adin sa ya ɗora Uba Sani a matsayin mGajin sa.

Sai dai kuma da yawa daga cikin masu yi wa siyasar Kaduna fashin baki ba su ɗauka hakan za ta faru tsakanin gwanayen biyu a wannan lokaci da mulki ba ta shekara ba.

Uba Sani a wani taro a Kaduna ranar Asabar ya bayyana cewa hatta albashi na yi masa wuyan biya ne saboda ɗinbin badhin da El-Rufai ya tattagi a lokacin da yake gwamnan jihar.

Sani Sani na jihar Kaduna ya bayyana cewa ya gaji bashin da ya kai $587m, N85bn da kuma bashin kwangiloli 115 daga gwamnatin da ta shude ta Nasir El-Rufai, inda ya koka da yadda a dalilin bashin ko an turo wa jihar kudi daga asusun tarayya ba ta samun wani abun kirki.

Sai dai kuma bayan kammala wannan taro, ɗan El-Rufai, Bashir El-Rufai a shafinsa ta X ya maida wa gwamnan da martani inda ya ce ” Maimakon Uba sani ya kawai fito fili ya nuna ya gaza, ya boye bayan wai bashin da aka ciwo ne wai yake haba shi aiki a jihar.

” Kawai waɗannan mutanen sun gane ba za su iya wa mutane komai ba ne sai suke karkata zuwa wani abun.

” Daga gwamnan su wanda ya maida ofishin sa Abuja, sai tarin ƴan yuyuyu da ya naɗa wai mataimakan sa, kawai don ya saka musu a siyasance, maimakon naɗa fitattu, kwararru, gogaggu, ya fake da an ciwo bashi ba ya komai.

People are also reading