Home Back

Mamakon ruwan sama ya ruguje fiye da gidaje 100 a jihar Jigawa.

dalafmkano.com 2024/7/3

Wani mamakon ruwan sama haɗe da guguwa da aka yi a wasu garuruwa da ke karamar hukumar Kaugama a jihar Jigawa, ya yi sanadiyyar rushewar fiye da gidaje sama da 100 a jihar.

A zantawar wakilinmu Abubakar Sabo, da guda daga cikin ‘yan kungiyar samar da ci gaban karamar hukumar da al’amarin ya faru, mai suna Haruna Kani Kaugama, ya ce, bayan faruwar al’amarin a ranar Talatar da ta gabata, ya tattara bayanan akalla mutane 72, da gidajensu suka ruguje, lamarin da ake ci gaba da tattara bayanan.

Haruna Ƙani, ya kuma yi kira ga mahukunta da su kai wa al’ummar karamar hukumar ta Kaugama da ke jihar Jigawa, da al’amarin ya faru da
su ɗaukin da ya kamata bisa dumbin asarar da suka yi, baya ga batun halin talauci da al’ummar yankin suke ciki.

“Ko nima sai da wani ɗakina ya ruguje kuma har kawo yanzu da nake muku wannan bayanin ban iya samun damar gina shi ba bisa halin babu da muke ciki, “in ji shi”.

Sai dai a nasa bangaren babban Sakataren hukumar ba da agajin
gaggawa ta jihar Jigawa SEMA, Dakta Haruna Mairiga, ya ce tuni
hukumarsu ta tura tawagar da za ta tantance irin barnar da aka samu tare da bayar da tallafi ga wadanda abin ya shafa.

Wannan dai na zuwa ne bayan da ko a baya ma irin Ifrila’in ya faru a garin Fagam da ke ƙaramar hukumar Gwaram, da kuma wasu sassan ƙaramar hukumar Ringim, dukka da ke jihar ta Jigawa.

People are also reading