Home Back

Mataimakin Gwamnan Kebbi Ya Nisanta Kansa Da Kiran PDP Na A Miƙa Masa Ragamar Mulkin Jihar

leadership.ng 2024/7/2

Mataimakin gwamnan jihar Kebbi, Sanata Umar Abubakar Tafida, ya nesanta kansa da sanarwar da jam’iyyar adawa ta PDP ta fitar na neman a miƙa ragamar mulkin jihar ga hannunsa biyo bayan gwamnan jihar na shirin tafiya aikin Hajji 2024.

Jam’iyyar PDP ta fitar da sanarwa a ranar Laraba 5 ga watan Yuni a Birnin Kebbi inda ta bukaci Gwamnan Jihar da ya mika ragamar mulki ga Mataimakin Gwamna a daidai lokacin da yake shirin tashi zuwa kasar Saudiyya domin gudanar da aikin Hajjin bana.

PDP ta kafa hujja da sashe na 190(1)(2) na kundin tsarin mulki.

A martanin da Mataimakin Gwamnan, Sanata Umar Abubakar-Tafida ya mayar, ya ce ko da yaushe Gwamnan Jihar yana mika mulki ga mataimakinsa ko da tafiyar yini daya yayi ba ya jihar ko.

“Mun yi mamakin da’awar da ‘yan adawa ke yi na Mika ragamar Mulkin Jihar ga mataimakinsa”. Domin ko da rana daya Gwamna Nasir Idris bai taba hanani yin aiki ba, Inji mataimakin Gwamna Santa Umar Abubakar- Tafida a yayin taron manema labaru da ya kira a gidansa da ke Birnin Kebbi.

“Domin kaucewa shakku, jihar Kebbi na da banbanci a tsakanin dukkan jihohin Nijeriya inda kyakkyawar alaka ta aiki da juna tsakanin gwamna da mataimakinsa, har ma da sauran majalisar zartarwa”.

“Muna fatan kuma muna addu’a cewa mafi kyawu da kyakykyawan dangantakar aiki da ke tsakaninsu ta ci gaba da dorewa domin amfanin al’ummar jihar Kebbi,” mataimakin ya bayyana haka ne a lokacin da yake ganawa da manema labarai a gidansa da ke Birnin Kebbi a ranar Alhamis din nan.

People are also reading