Home Back

Kungiyar Kwadago Na Shirin Yin Watsi Da Kari Kadan Kan 60,000 A Kan Mafi Ƙarancin Albashi

leadership.ng 2024/7/1
Kungiyar Kwadago Na Shirin Yin Watsi Da Kari Kadan Kan 60,000 A Kan Mafi Ƙarancin Albashi 

Shugaban Kungiyar Kwadago ta TUC, Festus Osifo, ya sha alwashin yin watsi da Naira 60,000 a matsayin mafi karancin albashin ma’aikata.

A ranar Talata ne kungiyar kwadagon NLC da TUC suka dakatar da yajin aikin da suka fara a ranar Litinin, biyo bayan alkawarin da gwamnati ta yi na yin kari a kan mafi karancin albashin Naira 60,000.

Yayin wata hira a gidan talabijin na Channels a ranar Talata, Mista Osifo ya ce: “A taron da suka yi a ranar Juma’a, (kwamitocin uku) sun ce ba za su kara wani abu a kan Naira 60,000 ba amma a taron jiya (Litinin), shugaban kasa ya ce zai yi kari a kan 60,000.”

Da aka tambaya shi kan ko kungiyar za ta amince da karin wasu ‘yan tsirarun kudi, ya ce sam kungiyar ba za ta lamunci hakan ba kuma a shirya ta ke ta yi watsi da duk wani kari mara ma’ana.

Mista Osifo ya ce kungiyar ba ta kayyade Naira 494,000 a matsayin sabon mafi karancin albashin ma’aikata ba, ta yi hakan ne don tsagin gwamnati ya nuna muhimmancin batun don cimma matsaya.

Ko da yake bai bayyana nawa kungiyar kwadagon ke so a matsayin mafi karancin albashin ba.

Ya kuma caccaki Babban Lauyan Tarayya kuma Ministan Shari’a, Lateef Fagbemi, kan bayyana hukuncin da kungiyar ta dauka a matsayin rashin tunani.

Shugaban TUC ya ce kungiyar ta bai wa gwamnatin tarayya wa’adin wata guda kafin shiga yajin aiki, wanda ya fara aiki daga ranar 1 ga watan Mayu, 2024, kuma ya kare a ranar 31 ga watan Mayu, 2024.

Shugaban na TUC ya ce burin kungiyar ya cika, domin yajin aikin na sama da sa’o’i 24 ya nuna yadda kowa ya gano muhimmancin ma’aikata a fadin kasar nan.

People are also reading