Kano: KEDCO ya Yanke Wutar Lantarkin Jami'ar Aliko Dangote Saboda Taurin Bashi
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano- Hukumar jami'ar kimiyya da fasaha ta Aliko Dangote da ke Wudil ta shiga tsilla-tsilla bayan kamfanin rarraba hasken wuta, KEDCO ya yanke masu wuta.
Baki daya jami'ar, wanda mallakin gwamnatin jiha ce ta shiga duhu saboda gazawarta wajen biyan kudin wuta da ake bin ta bashi.
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa mahukuntan jami'ar sun iya biyan N20m daga cikin N60m da KEDCO ke binta, inda kamfanin ya yanke shawarar yanke wutar kawai.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Da yake sanar da halin da ake ciki ga manema labarai a Litinin nan, shugaban sashen kula da kula da harkokin dalibai na jami’ar, farfesa Abdulkadir Dambazau, ya ce sun dogara ne kan wutar KEDCO.
Farfesa Dambazau ya jaddada cewa yanke wutar ya jefa baki daya jami'ar cikin damuwa ganin yadda ba su da hanyar samun haske.
Ya ce jami’ar na bakin kokarinta wajen biyan kudin wuta daga Naira miliyan 16 zuwa 17, sai kamfanin KEDCO ya kara zuwa Naira miliyan 50, baya ga bashin da suke kokarin biya.
Yanzu haka jami'ar na tunanin ko da a rufe jami'ar, ko a bar dalibai su ci gaba da karatu da zaman makaranta a cikin tsananin duhu.
A baya kun samu labarin yadda kamfanin rarraba hasken wutar lantarki na KEDCO zai fara yanke wutar wandanda suka hana shi kudin wuta.
Shugaban sashen yada labarai na kamfanin, Ibrahim Shan Shawar ne ya bayyana haka, kuma abokan huldarsa da ke Kano, Katsina da Jigawa lamarin zai shafa.
Asali: Legit.ng