Home Back

Shugaba Tinubu Na Shirin Gabatar da Ƙarin Kasafin Kuɗin 2024 a Majalisar Tarayya

legit.ng 2024/7/3
  • Bola Ahmed Tinubu na shirin gabatar da ƙarin kasafin kudin 2024 ga majalisar wakilan tarayya nan ba da jimawa ba
  • Shugaban ƙasar ne ya bayyana haka a jawabinsa ga mambobin majalisar yayin zaman haɗin guiwa ranar Laraba, 29 ga watan Mayu
  • Wannan na zuwa ne yayin gwamnatin Bola Tinubu ke cika shekara guda da kafuwa bayan karɓar mulki a watan Mayun 2023

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

FCT Abuja - Nan ba da jimawa ba Shugaba Bola Ahmed Tinubu zai gabatar da karin kasafin kudin 2024 ga majalisar dokokin kasar nan (NASS). 

Shugaban ƙasar ne ya bayyana haka yayin da yake jawabi a zaman haɗin guiwa a zauren majalisar datttawa ranar Laraba, 29 ga watan Mayu, 2024.

Shugaba Bola Tinubu.
Bola Tinubu na shirin miƙa daftarin ƙarin kasafin kudin 2024 ga majalisar tarayya Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu Asali: Facebook

Kamar yadda Channels tv ta ruwaito, Shugaba Tinubu ya ce:

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

"Na kawo maku kasafin kuɗi a baya kuma kun amince da shi. Yanzu haka muna kan aiki nan ba da jimawa ba zan kawo daftarin (ƙarin) kasafin kuɗin 2024."

A martanin da ya mayar, shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio, ya ce:

"Mun gode mai girma shugaban kasa, za mu yi dakon karin kasafin kudi na 2024 da wuri-wuri."

Har ila yau, a wurin zaman hadin gwiwa wanda ya yi daidai da cikar gwamnatin Tinubu shekara ɗaya, shugaban kasar ya tabbatar da sauya taken Najeriya.

Shugaban ya roki majalisar dattawa da ta wakilai da su ci gaba da aiki tare, su hada kai da gwamnati wajen gina kasar nan a kan turbar ci gaba mai dorewa.

"Bamu da wani zaɓi, kasar mu ce, babu wanda zai zo ya taimaka mana idan bamu tashi mun taimaki kanmu ba. Duk wani agaji da zai zo daga ƙasashen waje, sai da suka fara daga kansu.

"Don haka ya kamata mu haɗa kan mu wuri ɗaya mi gina kasar nan kamar yadda muka fara, ba don kan mu kaɗai ba, har da jikokin mu masu zuwa."

A wani rahoton kuma majalisar wakilan tarayya za ta gudanar da bincike kan korar ma'aikata sama da 600 a babban bankin Najeriya (CBN).

Majalisar za ta binciki yadda aka yi aka rubutuwa ma'aikata akalla 600 takardar kora a CBN bayan ta amince da wani kudiri da aka gabatar.

Asali: Legit.ng

People are also reading