Home Back

Kwamishinan ƴan sanda ka gaggauta cafke tsohon sarkin Kano Aminu Ado Bayero a duk inda yake – Gwamnatin Kano

dalafmkano.com 2024/6/29

Gwamnatin jihar Kano ta umarci Kwamishinan ƴan sandan jihar CP Muhammad Usaini Gumel, da ya gaggauta kama sarkin Kano na 15, da aka sauke Alhaji Aminu Ado Bayero, a duk inda yake ba tare da ɓata lokaci ba.

Gwamnan Kano Injiniya Abba Kabir Yusuf, ne ya bayar da umarnin kama Alhaji Aminu Ado Bayero, da safiyar Asabar ɗin nan, bayan da ya shigo Kano, inda gwamnatin ta zarge shi da ƙoƙarin tayar da tarzoma tare da haifar da fitina a jihar.

Ta cikin wata sanarwar da babban daraktan yaɗa labaran gwamnan Sunusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar aka aikowa Dala FM Kano, da safiyar yau.

Sanarwar ta ce, gwamna Abba Kabir, ya ɗauki matakin umarnin kama Aminu Ado, ne bisa zargin sa da yunƙurin tayar da hankali a jihar Kano, domin daƙile yunƙurin da yake na tada tarzoma.

A ranar Alhamis ne dai majalisar dokokin jihar Kano ta rushe sarakuna biyar a fadin jihar, kuma ciki har da Sarkin Kano na 15 Alhaji Aminu Ado Bayero, baya da Majalisar ta yi wa dokar naɗa masarautun kwaskwarima, inda bayan sanya hannu gwamna Abba Kabir ya mayar da Mallam Muhammadu Sunusi na biyu, a matsayin sarkin Kano na 16.

People are also reading