Home Back

Yadda gwamnatin jihar Gombe ta karya farshin taki ga manoma

bbc.com 2024/10/5
.

Asalin hoton, Inuwa Yahaya

Yayin da damuna ta fara kan kama a Najeriya, gwamnatin jihar Gombe ta fara ɗaukar matakan samar wa da manoma a jihar takin zamani a farashi mai sauki.

Gwamnatin dai ta siyo kowan ne buhun na takin kan naira dubu Arba'in da biyar yayin da ita kuma ta ke siyarwa da manoman jihar takin kan naira dubu ashirin da biyu.

Barista AbdulLahi Jalo, wanda shi ne shugaban kwamitin rabon takin a jihar ta Gombe, ya shaida wa BBC cewar ana ci gaba da siyar da takin, wanda kuma an rage kashi hamsin ne daga ainhin yadda yake.

"Shugabanin kannan hukumomi a jihar ne ke jagorantar raba takin, da sai wakilan masarauta, da na mata da matasa, da jam'an tsaro" inji shi.

Barista Jalo ya musanta wasu rahotanni da ke cewa takin da suke raba wa wanda gwamnatin ƙasar ta ba wa jihohi ne domin su ba wa manomansu a kyauta.

A cewrsa gwamnatin jihar ce ta sayo shi musamman domin saukaka wa manoman jihar da kuma bunkasar ayyukan noma.

"Wanda ake zargi takin gwamantin tarayya ne na NGKS ne, ba a fara raba shi ba ma, duk da cewar ya zo Gombe, amma kafin nan ma ai gwamantin Gombe ta saba siyo taki ta rabawa manoman kayauta, ba tun yanzu ba" inji Barisata Jalo.

Ya nanata cewa "Kowacce ƙaramar hukuma da ke Najeriya akwai shugabancin ƙungiyar manoma, sannan akwai mai unguwa da dagaci, wanda dukkansu sun san manoman gaskiya da na bogi, shi yasa muka yi imanin cewa manoman ne za su ci gajiyar tallafin gwamantin Najeriyar" inji shi.

Najeriya dai na fama da matsin tattalin arziki da tsadar rayuwa da hauhawar farashin kayan amfanin yau da kullum musamman na abinci, duk kuwa da noman da ake yi a kasar.

A ɓangare guda kuma matsalar tsaro da ake fama da ita musamman a wasu jihohin arewacin ƙasar na tilasta wa manoma haƙura da zuwa gona, saboda tsoron kar 'yan bindigar su cutar da su.

People are also reading