Home Back

Kano Pillars Ta Kasa Zuwa Taka Leda Saboda Rashin Kuɗi

leadership.ng 2024/5/2
Tsohon Dan Wasan Kwallon Kafa Na Kano Pillars, Kofarmata, Ya Rasu

Ƙungiyar ƙwallon ƙafar Kano Pillars ta gaza zuwa jihar Abia, domin buga wasan gasar firimiyar Nijeriya tsakaninta da takwararta ta Enyimba International ta garin Aba, da ke jihar Abia. 

Wasu rahotanni sun bayyana cewa, ƙungiyar ba ta da kuɗin da za ta yi jigilar ƴan wasanta da masu koyarwa zuwa jihar ta Abia.

Wata majiya ta tabbatarwa da LEADERSHIP HAUSA cewa, rashin kudi ne ya hana ƙungiyar tafiya buga wasan kuma daman a lokuta da dama ƙungiyar tana karɓar aron kuɗi domin tafiya buga wasa a waje amma a wannan karon ta gaza samun bashin kuɗin.

Kano Pillars dai tana mataki na shida a kan teburin gasar firimiya ta Nigeria da maki 41 bayan buga wasanni 27.

Matsalar rashin kuɗi dai a wajen ƙungiyoyin ƙwallon kafa a Nigeria ba sabon abu bane, inda ko a wannan kakar an ɗage wasan Kano Pillars ɗin da Abia Warriors saboda matsalar kuɗi da Abia ta shiga, sannan an ɗage wasan Gombe United da Remo Stars shima saboda rashin kudi a hannun ƙungiyar ta Gombe United.

Wasan dai an shirya za a buga a ranar larabar nan mai zuwa, to sai dai zuwa yanzu kungiyar kwallon ƙafar kano Pillars din ta aikewa da hukumar da ke kula da Firimiyar Nijeriya (NPFL) takardar neman dage wasan.

People are also reading