Home Back

Me ya sa matasan Kenya ke zanga-zanga?

bbc.com 2024/10/5

Asalin hoton, Reuters

 Matasa a Kenya ke jogarantar zanga-zangar matsin rayuwa
Bayanan hoto, Matasa a Kenya ke jogarantar zanga-zangar matsin rayuwa
  • Marubuci, Basillioh Rukanga
  • Sanya sunan wanda ya rubuta labari, BBC News, Nairobi

Zanga-zanga kan wani sabon ƙudirin dokar ƙara kuɗaɗen haraji ya haddasa mutuwar mutum biyar a Kenya, abin da ya kai ga an ƙona wani sashi na ginin majalisar dokokin kasar.

Masu boren na cewa dokar za ta ƙaƙaba biyan haraji mai yawa kan talakawa da ƴan kasuwa da ke fuskantar durƙushewa saboda matsin tattalin arziki da hauhawar farashi.

Ƴansanda sun rinƘa harbi a ƙoƙarin tarwatsa masu boren a ranar Talata, wanda ya haifar da mutuwar mutane da dama da jikkata ɗaruruwa.

Gwamnati ta jingine wasu daga cikin abubuwan da suka tunzura wannan bore a ƙudirin, sai dai bukatar masu zanga-zangar ita ce a soke batun dokar baki ɗaya.

Me ƙudirin ya kunsa?

  • Haraji kan kayan amfanin yau da kullum

Kudirin dokar ya bukaci a bijiro da tsarin biyan kashi 16 cikin 100 na kuɗin duk cinikin da aka yi kan burodi a matsayin haraji da kuma kashi 25 cikin 10 kan man girki.

Sannan akwai shirin karin kudin harajin tura kudade tsakanin bankuna da kuma sabon harajin shekara-shekara kan motoci wanda ya kai kashi 2.5 cikin 100 na darajar motar mutum.

Sai dai kalubalantar kudirin daga wajen al'umma, ya tilasta wa gwamnatin soke wannan batu.

  • Harajin muhalli

Kudirin zai sa haraji mai tsanani kan kayayyakin da ke gurbata muhalli, wani abu ne da ya haifar da ce-ce-ku-ce abin da ya sa gwamnati a yanzu ke maganar a sassauta.

Masu suka sun ce wannan mataki zai haifar da tsadar kayayyakin amfanin yau da kullum irinsu audugan mata. Sun ce akwai yara mata da dama da yanzu haka ma ba sa iya sayen audugan, yanayin da ke hanasu zuwa makaranta a lokacin haila.

Wannan zai kuma shafi farashin gunzugun jariai.

Gwamnati ta ce harajin zai shafi kayayyaki ne da ake shigowa da su daga ketare.

Harajin muhalli ya kuma shafi kayayyakin fasaha, irinsu wayoyin hannu da kyamarori da na'urar nadar magana ko hotuna.

Amma 'yan Kenya da dama na cewa sun dogara kan wadannan kayayyaki, masu muhimmanci ga bunkasar tattalin arzikin fasaha, domin rayuwa.

Wani fannin ne haraji zai fi tasiri?

  • Haraji kan asibitoci masu kwarewa

Kudirin ya bijiro da tsarin biyan harajin kashi 16 cikin 100 kan bukatun yau da kullum na kai tsaye ko a hade a harkokin gini da sayen kayayyakin amfani a asibitoci da ke daukan mutane 50.

'Yan Kenya da dama na nuna damuwa cewa wannan na iya ta'azara kudin kula da lafiya.

Shugaban kwamitin harkokin kudade, Kuria Kimani, ya yi watsi da batun da mutane ke yi cewa kudirin zai tsawwala kudaden asibiti ga masu fama da kansa.

  • Harajin shigo da kayayyaki

Kudiri ya bukaci a kara kudaden harajin shigo da kayayyaki daga kashi 2.5 cikin 100 zuwa kashi 3 na yawan kayayyakin da aka shigo da su.

Wannan kari na zuwa ne shekara guda bayan rage harajin daga kashi 3.5 cikin 100 zuwa kashi 2.5.

Masu zanga-zangar na cewa canji zai tsawwala ko haifar da tsadar kayayyakin da ake shigowa da su.

Asalin hoton, Getty Images

Masu zanga-zangar na cewa ana tsawwala 'yan Kenya haraji, yayin da shugaban kasar ke nuna ba gaskiya ba ne
Bayanan hoto, Masu zanga-zangar na cewa ana tsawwala 'yan Kenya haraji, yayin da shugaban kasar ke nuna ba gaskiya ba ne

Me ke ta'azzara zanga-zangar?

A ranar Talata, 'yan majalisa suka amince da kudirin, duk da cewa sun jingine wasu abubuwan da ke haifar da cece-kuce.

Masu zanga-zangar sun tumbuke shinge da 'yan sanda suka kafa tare da farwa ginin majalisa, da cinna wuta a wani bangare na ginin.

Kasashen yammaci sun nuna matukar damuwarsu kan abubuwan da ke faruwa tare da kiran a kwantar da hankali.

Shugaba William Ruto a baya ya alkawarta gabatar da jawabi domin shawo kan masu boren.

Me ya fusata masu zanga-zangar?

Duk da cewa gwamnati ta ajiye wasu daga cikin abubuwan da ke kunshe a kudirin, akwai wasu da ba a cire ba, ciki harda batun haraji mai yawa kan kayayyakin da aka shigo da su kasar.

Amma akwai damuwar da ta wuce batun wannan kudiri. Fusatatun 'yan Kenya na nuna matukar fushinsu da gwamnati da suke ganin ta jima tana watsi da kokensu.

Sai dai Mista Ruto ya gaggara gamsar da masu boren, yana cewa harajin da 'yan Kenya ke biya bai kai a kwatanta da wasu kasashen Afirka ba.

Ko a bara sai da aka gudanar da irin wannan bore lokacin da aka bijiro da makamancin wannan kudiri na haraji.

Me zai faru a nan gaba?

Yanzu dai majalisa ta amince da kudirin. Shugaban kasa na da zabin sanya hannu a kan ta zama doka nan da kwanaki 14 ko kuma ya mayar da shi gaban majalisa domin sake zaman gyara da kwaskwarima.

Gwamnatin na kuma iya bijiro da wasu tsare-tsare domin rage radadin da ake ciki ko matsi, ciki harda sauya kudirin ko jingine wasu abubuwan.

People are also reading