Home Back

An Zaɓi Dalibai Domin Samun Lamunin Karatun NELFUND, Gwamnati Ta Bayyana Adadinsu

legit.ng 2024/10/5
  • Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya bayyana adadin daliban da gwamnati ta zaɓa domin samun lamunin karatu
  • Sanata Godswill Akpabio ya ce daliban sune karon farko da za su fara cin gajiyar shirin da shugaba Bola Tinubu ya kawo na NELFUND a Najeriya
  • Har ila yau, Sanatan ya yi karin haske kan wasu kudurorin doka da majalisar dattawa ta kawo a karkashinsa wanda suna da matukar amfani ga kasa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya yi albishir ga daliban da suka nemi lamunin karatun NELFUND.

Shugaban majalisar ya bayyana cewa a halin yanzu an kammala zaɓen daliban da za suci moriyar shirin a karon farko.

Bola Tinubu
Sanata Akpabio ya bayyana adadin daliban da za a ba lamunin NELFUND. Hoto: @Dolusegun Asali: Twitter

Jaridar Leadership ta ruwaito cewa Sanata Godswill Akpabio ya bayyana haka ne a jiya Talata, 18 ga watan Yuni.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

NELFUND: Adadin daliban da ka zaɓa

Shugaban majalisar dattawa, Sanata Godswill Akpabio ya bayyana cewa an zaɓi dalibai sama da 30,000 cikin dimbin dalibai da suka nemi lamunin NELFUND.

Sanata Godswill Akpabio ya ce samar da lamunin yana daga cikin abin da yake faranta masa rai kasancewar an samar da shi a karkashin jagorancinsa a majalisa.

Amfanin lamunin NELFUND ga dalibai

Sanata Godswill Akpabio ya ce bayar da lamunin NELFUND zai taimaka matuka ga talakawa wajen samun damar zurfafa karatu, rahoton Nairametrics.

Sanatan ya ce saboda ba yan kasa damar karatu ba tare da bambanci ba shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya ƙirƙiro shirin.

Amfanin canza taken Najeriya

Sanata Godswill Akpabio ya bayyana cewa canza taken Najeriya da aka yi yana da muhimmanci sosai ga zaman lafiya.

Akpabio ya ce da tun farko an canza taken da ya sanyawa yan kasa kishi ta yadda ba za a samu masu ayyukan ta'addanci da garkuwa da mutane ba.

Iyaye sun koka kan NELFUND

A wani rahoton, kun ji cewa iyaye da ɗalibai sun koka a kan kwaskwarimar da gwamnatin tarayya ta yi wa sabon tsarin ba da lamuni ga dalibai.

Shugaban kungiyar daliban jami'a ta kasa (NAUS), kwamared Obaji Marshall, ne ya magantu a kan canje-canje da gwamnati ta yi a cikin shekarar 2024.

Asali: Legit.ng

People are also reading