Home Back

GOBARA DAGA KOGI: EFCC ta ɓallo wa Yahaya Bello ruwan zafi, ta saka sunan sa cikin harƙallar kuɗaɗen da aka gurfanar da ƙanin sa

premiumtimesng.com 2024/4/29
SABUWAR RIGIMA A APC: Ba zan janye daga takara ba, zan ragargaza APC idan aka cire suna na -Yahaya Bello

Hukumar EFCC ta bayyana wa kotu cewa tsohon Gwamnan Kogi, Yahaya Bello na da masaniya da kuma hannu a cikin harƙallar da ta gurfanar da wani ƙanin Yahaya ɗin mai suna Ali Bello da wasu mutane, bisa zargin wawurar maƙudan kuɗaɗe, a Babbar Kotun Tarayya da ke Abuja, a ranar Alhamis.

EFCC ta yi wa canje-canjen da ta ke wa waɗanda ta gurfanar ɗin a ranar 5 ga Fabrairu, daga caje-caje 10 zuwa 17 kan Ali Bello da Dauda Suleiman, s shari’ar da aka fara tun cikin 2022.

Mai gabatar da ƙara daga EFCC ya bayyana wa kotu cewa tsohon Gwamnan Kogi, Bello a ɗaya daga cikin waɗanda aka ƙara shigo da su waɗanda tuhuma ta hau kan su.

Tuhuma ta ɗaya dai a wurin ne kaɗai sunan Yahaya Bello ya fito. EFCC ta zarge shi da haɗa baki da Ali Bello, Dauda Suleiman da Abdusalam Hudu cikin Satumba 2015, suka karkatar da Naira biliyan 70, mallakar gwamnatin Jihar Kogi zuwa amfanin kan su.

EFCC ta bayyana cewa Hudu ya ari takalmin kare, ya tsere.

An zarge su da karkatar da Naira biliyan 100 ta gwamnatin Kogi, a lokacin da Bello ya na gwamnan Kogi.

Laluben Naira Biliyan 80 Cikin Aljifan Yahaya Bello: Gwamnatin Kogi Ta Ce EFCC Ta Kwarkwance, Ta Fara Bilumbituwa:

Tun cikin Fabrairu ne, ƙasa da kwanaki bakwai bayan saukar kan mulki, bayan ya shafe wa’adin shekaru takwas ya na Gwamnan Jihar Kogi, aka gayyaci Yahaya Bello domin gurfana kotu, domin tuhumar sa zargin karkatar da Naira biliyan 80 daga aljihun gwamnati zuwa aljifan sa.

Yahaya Bello ya miƙa mulki ga Usman Ododo a ranar 27 ga Janairu.

EFCC ba ta damu ta gabatar wa kotu wasu sabbin tuhume-tuhume a kan Bello ba, sai kawai ta yi kwaskwarima kan cajin tuhume-tuhumen da kotu ke wa wani ɗan uwan tsohon gwamnan da makusancin sa, waɗanda kotu ke tuhuma kan zargin karkatar da biliyoyin nairorin Jihar Kogi.

Abin da kawai EFCC ta yi shi ne ɗora tuhume-tuhumen da ake wa Yahaya Bello a cikin waccan shari’a da ke gaban kotu.

A shari’ar dai ana tuhumar ƙanen Yahaya Bello mai suna Ali Bello da wani mutum mai suna Dauda Suleiman da laifin karkatar da kuɗaɗe.

To amma a cikin shari’ar yanzu an haɗa da Yahaya Bello, wanda shi kuma aka tuhume shi da zargin karkatar da Naira biliyan 80 zuwa aljifan sa. Adadin kuɗaɗen da EFCC ke nema a hannun da sun kai N80,246,470,089.88.

Tuhume-tuhumen sun nuna cewa abokin jidar kuɗaɗen mai suna Abdulsalami Hud, wanda Jami’in Kula da Harkokin Kuɗaɗe ne Gidan Gwamnatin Jihar Kogi, ya cika wandon sa da iska, ya gudu.

To sai dai kuma tuni har sabuwar Gwamnatin Jihar Kogi ta yi wa EFCC zazzafan raddin cewa bulkara da hauragiya ta ke yi, domin laifukan da ake cajin Yahaya Bello da aikatawa, ta ce an yi su ne tun wajen Satumba, 2015, lokacin Yahaya Bello bai ma zama gwamna ba.

Kwamishinan Yaɗa Labaran Jihar Kogi, Kingsley Fanwo, wanda kuma shi ne dai kwamishinan yaɗa labarai a mulkin Yahaya Bello, shi ne ya fito da bayanin da ke ƙunshe da raddin da gwamnatin ta Jihar Kogi ta yi wa EFCC.

Mutane da dama na mamakin gaggawar maka Yahaya Bello kotu, alhali ga irin su Bello Matawalle, maimakon a gurfanar da shi kamar yadda EFCC ta zarge shi, sai na aka naɗa Ƙaramin Ministan Tsaro.

Haka tsohon Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje, shi ma maimakon a ji an ce EFCC ta yi cacukui da shi bayan saukar sa, sai ana naɗa shi Shugaban APC, jam’iyya mai mulki.

 
People are also reading