Home Back

JIRGIN TINUBU: Za a sayo wa Tinubu tsohon jirgin da Bankin Jamus ya ƙwace daga hannun wani Balarabe mai taurin-bashi

premiumtimesng.com 5 days ago
Tinubu ya tafi hutu Landan da Paris, daga can zai zarce Umrah

PREMIUM TIMES na da tabbacin cewa shi ma Jirgin Shugaban Ƙasa da ake ta haƙilon sayo wa Shugaban Ƙasa Bola Tinubu, tsoho ne, kuma daga wani Bankin Jamus za a sayi jirgin, wanda Bankin Jamus ya ƙwace daga hannun wani attajirin Balarabe mai taurin-bashi.

Jirgin dai samfurin Airbus A330 ne da aka ƙwace daga hannun Balaraben, wanda wani babban dillalin fetur ne da ya kasa biyan bankin wani bashin maƙudan kuɗaɗen da ya ke bin sa.

Sai dai jami’an Fadar Shugaban Ƙasa sun yi gum da bankin su, sun ƙi cewa komai, dangane da shirin sayo jirgin na shugaban ƙasa.

Amma kuma wannan jarida ta samu cikakken bayanin cewa gwamnatin tarayya tuni har ta zaɓo jirgin, amma a yanzu faɗi-tashin harhaɗa kuɗin biya ake yi domin a tabbatar da shigar ciniki.

Shi dai jirgin, wani Balarabe ne ya bayar da shi ajiya ga Bankin Jamus, a matsayin kadara, lokacin da zai karɓi bashi a hannun bankin, domin ya sayi jirgin.

A irin wannan ramce, daga lokacin da ka karɓi kuɗin ka sayi jirgin, to bankin zai karɓe jirgin idan ka kasa biyan kuɗin da ka ramta.

Majiyar PREMIUM TIMES ta ce jirgin dai ya zame wa Bankin Jamus alaƙaƙai, bayan bankin ya rasa mai sayen sa, saboda tsadar sa.

A yanzu dai jirgin ya na hannun kamfanin L & L International LLC, wani kamfanin hada-hadar cinikin jirage da ke birnin Miami, Jihar Florida, a Amurka.

Kamfanin L & L ɗin ne ke wa Bankin Jamus dillancin jirgin, ya na ƙoƙarin sayar wa gwamnatin Najeriya.

An ce jirgin dai irin na ƙasaitattun mutane ne, wanda aka ƙiyasta kuɗin sa zai kai Dala miliyan 600.

“Ciniki ya kakare yayin da Gwamnatin Najeriya ta yi wa jirgin mugun-tayi kan Naira Dala miliyan 100,” haka wata majiya ta tabbatar wa jaridar nan, kuma babu ma tabbatacin kamfanin L & L zai amince da wannan mugun-tayi.

Asarƙalar Ciniki Cikin Ciniki:

Wata majiya kuma ta shaida wa PREMIUM TIMES cewa, “idan har kamfanin L & L International ya sayar wa Najeriya jirgin a Dala miliyan 100, to Najeriya za ta iya sayar da shi nunki biyu na farashin da aka sayar mata da jirgin.

Bayanin Kamfanin L & L International Ga PREMIUM TIMES:

Kakakin Yaɗa Labaran L & L International ya shaida wa PREMIUM TIMES a ranar Alhamis cewa ba shi da cikakken bayanin yadda cinikin jirgin ke tafiya, wanda jaridar ta gano cewa tuni har Najeriya ta taya jirgin, an ce albarka.

Wata majiya kuma a kamfanin AMAC Aerospace AG na ƙasar Swiss, shi ne ke wa Najeriya dillacin sayo mata filin.

AMAAC Aerospace ne ke wa bargar Jiragen Fadar Shugaban Ƙasa garambawul tsawon shekaru da dama.

Majiya ta ce L & L ne ya samo labarin jirgin kuma ya labarta wa gwamnatin Najeriya, tare da bayar da shawarar ta sayi jirgin. Kamfanin ne ya tabbatar wa Najeriya cewa jirgin rangaɗau yake, garau ba shi da wata matsalar komai.

PREMIUM TIMES ta tuntuɓi Daraktan AMAC International, wato Daraktan Kula da Garambawul, Alexsis Ott, amma ya ƙi ya ce komai. Ya ce shi ba ya tattauna batun hada-hadar ciniki da wanda ba shi da hannu a cikin cinikin da kuma ya ke so ya san abin da ake ciki.

Majiyoyi daga Fadar Shugaban Ƙasa sun shaida wa PREMIUM TIMES cewa ana nan ana ta haƙilon yadda za a haɗa kuɗaɗen sayo jirgin. Yayin da ita kuma gwamnati ta sa jiragen shugaban ƙasa guda uku a kasuwa, amma kuma ta haƙƙaƙe cewa kuɗaɗen da za a yi gwanjon jiragen uku ko kaɗan ba za su kai kuɗin sayen wancan danƙareren jirgi mallakar Bankin Jamus ba.

People are also reading