Kawun Tsohon Ministan Najeriya, Farfesa Isa Pantami Ya Rasu Yana da Shekara 110
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Tsohon ministan Najeriya kan tattalin arziki na zamani, Farfesa Isa Ali Pantami ya sanar da rasuwar yayan mahaifiyarsa.
Farfesa Isa Pantami wanda ya yi minista a zamanin mulkin Buhari ya ce kawun nasa, Malam Abubakar Audu ya rasu yana da shekaru masu yawa a duniya.
Kamar yadda ya wallafa a shafinsa na X a yammacin yau Talata, Pantami ya ce Malam Abubakar ya rasu a garin Hausari, karamar hukumar Machina da ke jihar Yobe.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar sanarwar tsohon ministan:
"A yau kawun mu, yayan mahaifiyar mu, wato Malam Abubakar Audu wanda aka fi sani da suna Malam Dankule ya rasu.
"Allah ya dauki rayuwarsa a karamar hukumar Machina a garin Hausari da ke jihar Yobe a wurin da yake rayuwa."
Sanarwar Farfesa Pantami ta ƙara da cewa Malam Dankule ya koma ga Allah ya na da sama da shekara 110 a duniya bisa kiyastawar alƙaluma.
"Allah ya sa Aljanna Firdausi ce makomarsa sa sauran iyayen mu da malaman mu da zuriyar mu."
In ji Farfesa Pantami.
Ma'abota shafin X sun yi tururuwa wajen yi wa Pantami ta'aziyyar wannan rashi da ya yi.
@UmmUSerLMer:
"Allah ya gafarta mai."
@AjeeyaIk:
"InnalilLahi wa inna ilaihi raji’un. Allah ya kai haske kabarinsa. Makocinmu ne."
@jdeshikat:
"Allah ya gafarta masa. Allah ya kuma ya ba wa iyalai da abokanai hakurin rashin sa.
@Madawaki_Jr:
"Allah ya gafarta ma shi ya sa ya huta da duk sauran al’umar musulmi."
Asali: Legit.ng