Home Back

SHIRIN NOMA NA ACReSAL: Bankin Duniya ya bai wa ma manoma ramcen Naira miliyan 370 a Jigawa

premiumtimesng.com 2024/6/16
‘INKONKULUSIB’:  APC ta sha kasa a Jigawa, Yakubu na PDP ya yi nasara a zaɓen kujerar ɗan majalisar Tarayya

Bankin Duniya (World Bank), ya bai wa manoma lamunin Naira miliyan 370 a yankunan karkara 10 a faɗin Jihar Jigawa.

An bayyana sanarwar bayar da lamunin a ƙarƙashin Shirin Noma na ACReSAL.

Gwamna Umar Namadi ne da kan sa ya ƙaddamar da taron raba wa manoma ramcen kuɗaɗen, inda ya ke cewa wannan tallafin lamuni daga Bankin Duniya ya zo daidai lokacin da ya dace, domin gagarimar gudummawa ce ga gwamnatin sa a ƙoƙarin cimma nasarorin ajandojin gwamnatin guda 12, waɗanda ya yi kamfen da su kafin hawan sa mulki.

Gwamna Namadi ya bayyana cewa ƙara wa al’ummar yankunan karkara ƙwarin-gwiwar ƙarfafa harkokin kasuwancin su da kuma samar masu yanayin bunƙasa harkokin inganta rayuwar su, duk abubuwa ne da ke shimfiɗe a cikin ajandoji 12 na gwamnatin sa.

“Saboda haka wannan tallafin lamuni daga Bankin Duniya na daga cikin irin tsare-tsaren da waɗannan ajandoji suka ƙunsa.”

Namadi ya ce an zaɓi yankunan karkara 10 inda kowace wuri za a ba su Naira miliyan 37, waɗanda za a raba wa manoman da aka tantance, kuma su ke harkokin noman ka’in-da-na’in.

Gwamnan ya ce ya na da yaƙinin tabbas idan aka yi amfani da kuɗaɗen ya hanyar da ta dace a waɗannan yankuna 10, to za a samu gagarimin canjin da zai kawar da talauci, ya samar da aikin yi, bunƙasa abinci da kuma ci gaba a waɗannan yankuna.”

Da ya ke jawabi, Kwamishinan Raya Muhalli, Nura Ibrahim, ya bayyana cewa wannan lamuni da ake kira CRFs, an bijiro da shi ne domin tallafa wa manoman yankunan karkara, ta yadda za su yi noman amfanin gona wanda ke tafiya daidai da yanayi, wanda zai taimaka wajen samar da jari sosai a karkara da cikin gidajen al’umma.”

“Kowane rukunin manoma 10 zuwa 25, za a ba su Naira miliyan 37, kuma muna ƙoƙarin isa har ga rukuni na mutum 2,800 a faɗin Jihar nan.” Inji Nura.

Wata mace da ke cikin waɗanda suka karɓi lamunin mai suna Hajiya Iya Wawu, ya nuna godiya ga Gwamna Namadi, Bankin Duniya da kuma dukkan waɗanda suka taimaka wajen ganin wannan shiri ya yi nasara. Ita mata yi addu’ar samun nasarar shirin.

People are also reading