Hukumar Hisbah Ta Kwace Barasar da Aka Yi Niyyar Shiga da Ita Jihar Katsina
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Katsina - Hukumar Hisbah ta jihar Katsina ta ƙwace kimanin katan 142 na barasa da aka shirya kaiwa ƙaramar hukumar Daura.
Kwamandan Hisbah na jihar, Dakta Aminu Usman ne ya bayyana haka a wata hira da kamfanin dillancin labarai na Najeriya a Katsina ranar Asabar.
A cewar Aminu Usman, an kama barasar ne a ranar Litinin a yayin wani sintiri a faɗin birnin domin kawar da munanan ɗabi'u da rashin ɗa'a, cewar rahoton jaridar The Guardian.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwamandan na Hisbah ya bayyana cewa aikin ya kai ga kama motar da ke dauke da barasar a kan titin Ring Road na jihar, rahoton jaridar The Punch ya tabbatar.
Aikin ya gudana ne a ƙarƙashin kulawar Malam Nafi’u Ma’azu-Akilu, inda ya tabbatar da an kai kayan zuwa hedkwatar hukumar domin ci gaba da bincike.
Hakazalika, hukumar ta kuma gurfanar da wasu mata biyu a karo na huɗu a gaban kuliya bisa tuhumar su da laifin rashin ɗa'a.
Aminu Usman ya ce duk da gargaɗi da shawarwarin da aka yi ba su a baya, ƴan matan sun kasa gyara halayensu, lamarin da ya sa aka gurfanar da su a gaban kotun shari’ar musulunci.
A cewarsa, ƴan matan sun amsa laifinsu kuma an umarce a ci gaba da tsare su a gidan gyaran hali har zuwa ranar Alhamis domin ci gaba da shari’ar.
A wani labarin kuma, kun ji cewa hukumar Hisbah ta jihar Kano ta ƙwace kwalaben barasa aƙalla 8,600 da aka shake mota da su daga jihar Kaduna.
Jami'an hukumar sun riƙa bibiyar motar daga Kaduna har zuwa lokacin da ta shiga yankin jihar Kano sannan suka yi caraf da ita.
Asali: Legit.ng