Home Back

Za A Ci Gaba Da Amfani Da Na’urar BAR A Ingila

leadership.ng 2024/7/1
Za A Ci Gaba Da Amfani Da Na’urar BAR A Ingila

Gasar Premier League ta Ingila za ta ci gaba da amfani da na’urar tallafa wa alkalan wasa wadda aka fi sani da BAR a kakar wasa mai zuwa kamar yadda hukumomin gasar suka tabbatar.

An amince da matakin ne bayan da kungiyar kwallon kafa ta Wolbes ta kasance kungiya daya tilo da ta jefa kuri’ar amincewa da yin watsi da ita yayin ganawar shekara-shekara a ranar Alhamis.

Wolbes ce ta gabatar da kudirin kada kuri’ar cikin wani kundi da ta mika wa hukumar gasar a watan Mayu da ya gabata sai dai kafin a daina amfani da BAR din, akwai bukatar 14 cikin kungiyoyi 20 na Premier su kada kuri’ar amincewa da hakan, amma Wolbes ba ta samu goyon baya daga sauran kungiyoyi ba.

An dade ana matsa wa hukumar gasar ta gyara yadda ake amfani da na’urar, wadda aka fara aiki da ita a kakar 2019-2020, sannan an tabbatar yayin ganawar cewa za a kaddamar da wasu sabbin hanyoyin gano satar gida nan gaba kadan, yayin da hukumar ta ce za a dinga sanar wa ‘yan kallo dalilin da ya sa aka dauki mataki a cikin fili.

Ba da sanarwar daukar matakin da aka fara amfani da ita a gasar Kofin Duniya ta Mata ta 2023 na nufin alkalan wasa za su yi wa magoya baya bayani da zarar an gama amincewa da matakin da na’urar ta nuna.

People are also reading