Home Back

Majalisar Dattawa za ta gina katafaren asibiti don Sanatoci, Wakilan Tarayya, iyalan su da ma’aikatan su

premiumtimesng.com 2 days ago
DALA BILIYAN 18: Majalisar Dattawa ta kafa kwamitin binciken kwangilar gina Centenary City a Abuja

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ya bayyana cewa akwai shiri na nan a ƙasa wanda za a gina katafaren asibiti na zamani a Abuja, domin kula da lafiyar sanatoci, mambobin tarayya, baƙin su da kuma ma’aikatan majalisa.

Akpabio ya bayyana haka a ranar Alhamis, lokacin da ya ke maraba lale da sanatoci, bayan komawar su majalisa daga hutun da ya haɗa har da hutun Babbar Sallah.

Ya ce za a bai wa aikin ginin asibitin muhimmancin gaske a cikin shekara mai zuwa.

A yanzu haka dai akwai asibitin da ake duba lafiyar sanaticin da ‘yan majalisar tarayya ɗin. Amma duk da haka za su gina wani sabo katafare kuma na zamani.

“Mun yi tunanin gina wannan katafaren asibitocin ne domin kula da lafiyar mu sanatoci, mambobin tarayya da ma’aikatan majalisa.”

Daga nan kuma ya yi kira ga Sanatoci da su maida hankali sosai wajen ayyukan kula da lafiya, walwala da jin daɗin al’umma.

Za a gina wannan katafaren asibiti, wanda aka bijiro da batun sa a daidai lokacin da ake ta sa-toka-sa-katsi kan batun sayen jirgin Shugaban Ƙasa, wanda guda ɗaya zai ci maƙudan biliyoyin nairori.

Ana wannan cukumurɗar ce kuma a daidai lokacin da ake ka-ce-na-ce kan mafi ƙanƙantar albashi, wanda gwamnatin tarayya ta ce za ta iya biyan Naira 62,000.00, su kuma gwamnonin Najeriya suka ce ba za su iya biyan haka ɗin ba.

People are also reading