Su wane ne ba za su biya sabon harajin CBN ba?
A ranar Litinin ne Babban bankin Najeriya, CBN ya sanar da bijiro da tsarin cirar kashi 0.5 cikin ɗari a duk lokacin da aka tura kuɗi ta asusun banki da za a yi amfani da su wajen tabbatar da tsaro ta intanet.
A cewar bankin, matakin zai fara aiki ne nan da makonni biyu masu zuwa kuma ya ɓullo da tsarin domin magance barazanar laifukan intanet a tsarin hada-hadar kuɗi.
Sai dai tuni matakin ya tayar da ƙura a shafukan sada zumunta musamman a shafin X inda wasu ke nuna fushinsu kan yadda hukumomi ke ƙaƙaba jerin haraje-haraje a kansu.
CBN dai ya ce kuɗaɗen da aka cira daga asusun masu hulɗa da bankunan za a zuba su a asusun tsaron intanet na ƙasa wanda zai kasance a ƙarƙashin ofishin mai bai wa shugaban ƙasa shawara kan tsaro.
Duk da cewa CBN ya bijiro da harajin da ya janyo cece-ku-ce, bankin ya yi bayani cewa akwai waɗanda tsarin bai shafe su ba.
Ƙungiyar ƙoƙarin tabbatar da adalci ta SERAP ta nuna adawarta da sabon harajin na tsaron intanet.
Ƙungiyar ta buƙaci shugaban Najeriya Bola Tinubu da ya bai wa Babban Bankin Najeriya umarnin soke harajin kasancewar ya saɓa wa kundin tsarin mulkin Najeriya da kuma walwalar al'umma.
Wannan haraji zai zamo ɗoriya ne a kan jerin haraje-haraje da al'ummar Najeriya ke biya waɗanda Babban bankin ƙasar ya ƙaƙaba.
Cikin su akwai harajin kula da katin ATM, da kula da asusun ajiya, harajin gwamnati, cajin tura kuɗi daga wani banki zuwa wani da kuma harajin tura kuɗi ta laturoni.