Ministar Tinubu Ta Tafka Babban Rashi, Buhari Ya Kadu da Rasuwar da Aka Yi Mata
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Katsina - Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya tura sakon taa'aziyya kan rashin da Hajiya Imaam Sulaiman-Ibrahim ta yi.
Karamar Ministar harkokin 'yan sanda, Hajiya Imaan Sulaiman ta rasa mahaifyarta, Hajiya Aisha Danladi a jihar Nassarawa.
Sakon jajen na kunshe ne a cikin wata sanarwa da Buhari ya fitar a shafinsa na X a ranar Alhamis 27 ga watan Yunin 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Buhari ya ce marigayiyar ta kasance mace mai taimakawa al'umma da kuma iyalanta baki daya inda ya ce an yi babban rashi.
Tsohon shugaban kasa ya ce Minsitar ta rike masa mukamin daraktar hukumar NAPTIP lokacin da ya ke mulkin Najeriya.
Har ila yau, ya ce Imaan ta taba rike kwamishinar Tarayya a hukumar kula da masu gudun hijira a Najeriya.
Ya bukaci 'ya'yan da ta bari su yi su ci gaba da tabbatar da halayenta masu kyau domin ci gaban al'umma gaba daya.
Marigayiyar har ila yau, kafin rasuwarta, suruka ce ga Sanata Sani Musa da ke wakiltar Niger ta Gabas a Majalisar Tarayya.
A wani labarin, kun ji cewa mataimakin shugaban kasar Najeriya, Kashim Shettima ya rasa surukarsa a jihar Kano a makon da ya gabata.
Marigayiyar mai suna Hajiya Maryam Abubakar Albishir ta rasu ne a makon da ya gabata bayan ta sha fama da jinya na tsawon lokaci.
Marigayiyar mai shekara 69 a duniya ta rasu ne a birnin Kano a ranar Lahadi, 23 ga watan Yunin 2024 inda manyan mutane a ƙasar suka yi sallar jana'izarta..
Asali: Legit.ng