Home Back

Bayan Abin da Ya Faru a Delta 'Yan Ta'adda Sun Sake Yi Wa Sojoji Kwanton Bauna, An Rasa Mutum 6

legit.ng 2024/5/10
  • Ƴan ta'addan Boko Haram sun yi wa sojojin Najeriya kwanton ɓauna a jihar Borno yayin da suke kan hanyarsu ta shiga jihar Yobe
  • Mugayen ƴan ta'addan sun hallaka sojoji shida tare da raunata wasu bayan sun far musu a ƙauyen Kamuya
  • Wannan harin dai na zuwa ne kwanaki kaɗan bayan an yi jana'izar sojojin da ƴan ta'adda suka kashe a jihar Delta a wani kwanton ɓauna

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Borno - Aƙalla sojoji shida ne suka rasa rayukansu a wani harin kwantan ɓauna da aka kai musu a hanyar Biu-Buni Yadi a jihar Borno.

Sojojin sun mutu ne dai mako guda bayan da aka yi jana’izar sojojin da aka kashe a lokacin da suke aikin wanzar da zaman lafiya a jihar Delta a maƙabartar sojoji ta ƙasa da ke Abuja.

'Yan ta'adda sun hallaka sojoji
'Yan ta'addan Boko Haram sun hallaka sojoji a Borno Hoto: @HQNigerianArmy Asali: Twitter

Ta wace hanya ƴan ta'addan suka kai harin?

Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa mayaƙan Boko Haram sun yi wa sojojin kwanton ɓauna ne a Kamuya, wani ƙauye kusa da Buratai, mahaifar tsohon babban hafsan sojojin ƙasa, Laftanar Janar Tukur Buratai.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wata majiyar tsaro ta ce sojojin sun rasa ransu ne kan hanyarsu ta zuwa Damaturu domin sayen mai.

A kalamansa:

"Akwai matuƙar baƙin ciki, sun kasance sojojin 135 Special Force BN FOB a Buratai. An yi musu kwanton ɓauna a hanyarsu ta zuwa Damaturu, jihar Yobe, domin sayen mai."
"Abin takaici, mun rasa wani jami’i, direba, mai sarrafa bindiga da wasu ƴan rakiya huɗu, yayin da waɗanda suka jikkata ke asibiti suna karɓar magani."

An gwabza faɗa

Wani majiya mai tushe da ya tsallake rijiya da baya, ya ce yayin da yake kan hanyarsa ta zuwa garin Yadi, mahaifar Gwamna Mai Mala Buni na jihar Yobe, lamarin ya ritsa da shi.

A kalamansa:

"Ba zan iya kwatanta irin faɗan bindigar da aka yi ba, ƴan ta’addan da ke da yawa sun mamaye sojojin. Ikon Allah ne kawai ya sanya na tsira."

Kwamandojin ƴan ta'adda sun miƙa wuya

A wani labarin kuma kun ji cewa wasu manyan kwamandojin ƴan ta'addan ƙungiyar Boko Haram sun miƙa wuya a jihar Borno.

Ƴan ta'addan dai suna a ɓangaren ƙungiyar ne na Bakoura Badouma da ke a tsibirin yankin tafkin Chadi.

Asali: Legit.ng

People are also reading