Home Back

Jordan za ta yi taro na musamman kan agazawa Falasdinawa

dw.com 2024/7/6
Hoto: Habboub Ramez/abaca/picture alliance

Jordan za ta ka karbi bakuncin taro na musamman a Talatar nan kan hanzarta kai agajin jin-kai ga Falasdinawa, bayan Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin fadawar yankin cikin matsanacin halin yunwa, sanadiyyar shafe sama da watanni 8 ana yakin Gaza.

Taron dai na hadin gwiwa ne da Majalisar Dinkin Duniya da kuma Masar, kuma zai samu halartar jagoran Falasdinawa Mahmoud Abbas, tare da sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken, a ziyararsa ta 8 yankin Gabas ta Tsakiya tun bayan barkewar rikicin.

Ana sa ran taron zai mayar da hankali wajen kiran kasashen duniya da kungiyoyin agaji domin tallafawa Falasdinawan Gaza da ke fama da rashin abinci da ruwa da wutar lantarki.

People are also reading