Home Back

Abu huɗu da ya sa muke son cin zaƙi da yadda za mu kauce wa hakan

bbc.com 2024/5/9
...

Asalin hoton, Getty Images

Dukkan mu na son mu ci abu mai gina jiki, musamman idan muka duba burikanmu kan lafiya a farkon wannan shekarar.

Sai dai wasu lokutan ƙudurorin na fuskantar tangarɗa saboda kwaɗayin shan kayan zaƙi ko masu gishiri ko kuma abinci mai ɗauke da sinadaran gina jiki.

Hakan ne ya sa muke jin damuwa kan waɗannan kayan abinci lokacin da muke son inganta ci-makarmu ko rage ƙiba?

Kuma me za mu iya yi kan haka? Akwai dalilai da dama da ke sa kwaɗayin cin wasu nau'ikan abinci amma bari mu mayar da hankali kan fitattu guda huɗu:

Gagarumar raguwa a yawan sinadarin suga a jini

Sukari, wani muhimmin sinadarin ƙara kuzari ne ga duka dabbobi sannan ɗanɗanonsa ɗaya ne daga cikin abin daɗi da za ka ji.

Ko ba abubuwan da ke sa a ji ɗanɗano a baki, mutum na iya jin kwaɗayin shan abu mai suga, abin da ke nuna wata hanya da ta wuce batu na ɗanɗano.

Jijiyoyin da ke isar da saƙo idan an sha sukari suna fara aiki idan sukarin ya isa hanji.

Hakan na ƙara wa mutum kwaɗayi tare da saka ka ƙara shan abu mai suga. Yawan shan suga a duk lokacin da ka ji sha'awar hakan na ƙara kwaɗayin shan sukarin.

A dogon lokaci, bincike ya nuna abincin da ke da sinadarin suga da na iya shafar yanayin mutum da narkewar abinci da kuma kumburin hanji.

Yayin da ya kasance akwai bambanci a tsakanin mutane, yawan shan suga da abinci mai sinadaran gina jiki na ƙara yawan sukarin da ke cikin jini.

Idan sukarin da ke cikin jini ya ragu, jikinka na iya jin buƙatar samun sinadarin gina jiki galibi a yanayin suga da kayan abinci mai gina jiki saboda waɗannan na samar da hanya mafi sauri da sauƙi na samun nau'in kuzari.

Raguwar sinadaran 'dopamine' da 'serotonin'

Wasu sinadaran aike kamar 'dopamine' na lura da cibiyoyin samar da nishaɗi na ƙwaƙalwa. Shan sukari da abinci mai gina jiki na iya janyo fitar sinadarin dopamine, abin da ke haifar da daddaɗan yanayi da kuma ƙara sha'awar abu. Serotonin, sinadarin faranta rai na iya dankwafar da sha'awar cin abu.

Sauye-sauye a sinadarin serotonin na iya yin tasiri a sauyin yanayi da kuzari da hankali. Ana kuma alaƙanta hakan da yawan cin abinci mai gina jiki da rana. Abinci masu ƙarancin sinadarin carbonhydrate na iya rage serotinin tare da sauya yanayin mutum.

Sai dai wani bincike a baya-bayan nan ya nuna akwai alaƙa kaɗan tsakanin waɗannan nau'ukan abinci da kuma haɗarin shiga damuwa. Idan aka kwatanta da maza, mata sun fi jin sha'awar son cin abinci mai sinadaran gina jiki.

Shiga yanayin gajiya da damuwa ko kuma kwaɗayin cin abu mai sinadarin carbonhydrate na cikin alamomi na kafin zuwan jinin al'ada kuma ana iya alakanta shi da raguwar sinadaran 'serotonin'.

Rashin ruwa da raguwar suga da gishiri a jini

Wasu lokuta jikinmu na son abubuwan da ya rasa kamar ruwa ko ma gishiri. Abinci mai ƙarancin sinadaran gina jiki misali, yana rage yawan sinadaran insulin da rage yawan ruwan jiki.

Abinci mai ƙarancin sinaran gina jiki na haifar da "ketosis" - yanayin da jiki ke ƙona maiƙo domin saka kuzari maimakon suga. a matsayin hanyar samar da kuzari, nisanta daga yadda jiki ke dogara kan sinadaran carbonhydrate.

Ana yawan alaƙanta ketosis da ƙaruwar yin fitsari wanda ke bayar da gudummawa ga yiwuwar rashin ruwa da kuma kwaɗayin cin abu mai gishiri.

Ƙaruwar gajiya da rashin kwanciyar hankali

Gajiya da jin ba daɗi da saurin sauyin yanayi na iya janyo mutum ya ji sha'awar cin abincin da za su kwantar masa da hankali.

Saboda sinadaran da ke da alaƙa da gajiya na iya shafar son cin abincin mutum da zaɓin abinci. Sinadarin saka gajiya cortisol na iay janyo son cin abinci mai zaƙi.

Wani bincike a 2001 na mata 59 da ba su kai lokacin daina al'ada ba waɗanda suka fuskanci gajiya ya nuna cewa gajiya na janyo yawan cin abu mai sinadaran ƙara kuzari.

Wani bincike na baya-bayan nan ya gano cewa matsananciyar gajiya, idan aka haɗa da abincin da ke da yawan sinadaran ƙara kuzari, na ƙara yawan cin abinci da zaɓin abinci mai zaƙi.

Wannan ya nuna muhimmancin abinci mai gina jiki lokacin gajiya domin hana ƙara ƙiba.

Me za ka iya yi game da sha'awar son cin abu mai siga da ƙara kuzari?

Ga hanyoyi huɗu na shawo kan haka

1. Kar ka daina cin abincin da ya faɗo ƙarƙashin rukunan. Ka yi ƙoƙarin cin abinci mai gina jiki sannan ka tabbatar ka haɗa da abinci mai sinadarin protein domin taimaka maka ka ji ka ƙoshi da rage sha'awar son cin abu mai suga da abinci mai ɗauke da sinadarin carbonhydrate.

Ya kamata manyan mutane su yi ƙoƙarin cin tsakanin gram 20 da 40 na sinadarin protein cikin kowane abinci, musamman kan abincin safe da na rana sannan a rana yawan sinadarin da ya kamata mutum ya ci ya kai aƙalla ƙasa da gram ɗaya duk nauyin mutum domin lafiyar ƙwanji.

Abincin da ke da sinadarin fiber mai gina jiki kamar ganyayyaki da hatsi. Waɗannan na cika ciki da daidaita yawan sukarin da ke cikin jini. Misali kamar ganyen broccoli da shinkafa da wake da hatsi.

2. Lura da yanayin gajiyarka. Ka aiwatar da dabarun rage gajiya kamar yin numfashi a hankali da motsa jiki na yoga domin rage abin da ke iya tunzura sha'awar cin abinci. Yin taka tsan-tsan wajen cin abinci da cin abinci a hankali da gyara

3. Ka samu wadataccen barci. Ka samu akalla brci na sa'o'i bakwai zuwa takwas a kowane dare. rshin samun isasshen barci kan shafi sinadaran da ke motsa yunwa

4. Ka rika lura da adadin abincin d za ka ci. A duk lokacin da za ka ci abincin, ka rika lura da ywana abincin da za ka ci. Magance matsalar son cin siga da gishiri da abinci mai sa kuzari, yi kokacin cin abinci mai rai da lafiyatare da kokarin rage kiba babban kalubale ne.

Ku tuna cewa ana iya samun ci gaba ne da koma-baya a lokaci guda. don haka ka ksance mai hakuri.

People are also reading