Home Back

Minista: 'A Dawo da Betta Edu Domin Cigaba da Ayyukan Raya Kasa', An Roki Tinubu

legit.ng 2024/5/7
  • Wata kungiya mai zaman kanta ta roki shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya dawo da tsohuwar minista Betta Edu bakin aikin ta
  • Shugaban kungiyar Kayode Arimoro ya ce ya yi kiran ne lura da sakamakon binciken EFCC ya nuna ba a same ta da laifi ba
  • Ya kuma kara da cewa tsohuwar ministar ta fara ayyuka masu muhimmanci da ya kamata ta dawo ta karasa su domin cigaban kasa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Abuja - Watanni bayan korar da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya yi wa tsohuwar ministar jin kai, Betta Edu, wata kungiya ta yi kira domin dawo da ita.

Dr. Betta Edu
Shugaban kungiyar SNM Kayode Arimoro ya bukaci Tinubu ya dawo da Dr. Betta Edu. Hoto: @Edu_Betta @EFCC Asali: Twitter

Shugaban kungiyar mai zaman kanta (SNM), Kayode Arimoro ya roki shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya dawo da Betta Edu bakin aikin ta domin ta cigaba da ayyukan raya kasa da ta fara.

A cewar jaridar Leadership, mista Arimoro ya ce akwai abubuwan da suka jefa alamar tambaya ga lamarin da ya jawo korar ta daga aiki wanda ya kamata a wai-wai ce su.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa lamarin ya fara ne daga lokacin da tsohuwar ministar ta yi ƙoƙarin tura kudade ga ma su rangwamen karfi wanda kawai sai wasu suka maida lamarin abin zargi.

Hakan kuma ya kai ga kunnen hukuma mai yaki da yi wa tattalin arzikin kasa zagon kasa (EFCC) wanda daga bisani ya kai ga bincike.

Ya kara da cewa lamarin ya nuna lalle akwai bukatar sake nazari mai zurfi a kan harkar gwmanti ta inda ya kamata a samar da yanayi na gaskiya da rikon amana ba tare da wani ya jefi wasu da karya ba.

A binciken da EFCC ta yi kuwa, Arimoro ya ce shi ma binciken ya zo da alamar tambaya a kan irin matsalolin da suka yi wa harkar gwmanti dabaibayi.

Haka kuma ya kamata a kara sa ido a kan harkar gudanar da mulki a fadin ƙasar domin a magance irin matsalolin da suke nuna rauni a harkar aikin gwamnati.

Jaridar Vanguard ta ruwato cewa Arimoro ya kuma tabbatar da cewa binciken da EFCC ta yi bata samu Betta Edu da laifi ba, hakan kuma ya nuna irin gaskiyar ta da ya kamata shugaban ya duba yiwuwar dawo da ita aiki. Ga abin da yake cewa:

"Muna rokon shugaban kasa da ya duba yiwuwar mayar da ita bakin muƙamin ta domin ta cigaba da ayyukan masu kyau da ta fara"

-Kayode Arimoro, shugaban kungiyar SNM

EFCC ta kama da Betta Edu

A wani rahoton kuma, kun ji cewa ba tare da wani bata lokaci ba, Dr. Betta Edu ta burma hannun hukumar EFCC domin amsa tambayoyi

Edu ta zama ministar farko da Shugaba Bola Tinubu ya dakatar tun da ya rantsar da majalisar FEC watanni kadan da suka gabata

Asali: Legit.ng

People are also reading