Home Back

AIKI SAI MAI SHI: Gwamnatin Kebbi ta fara shirye-shiryen jigilar dawo da Alhazan jihar gida Najeriya

premiumtimesng.com 2024/7/2
AIKI SAI MAI SHI: Gwamnatin Kebbi ta fara shirye-shiryen jigilar dawo da Alhazan jihar gida Najeriya

Gwamnatin Kebbi ta bayyana cewa da zarar an kammala aikin Hajji a cikin mako mai zuwa za a fara kwashe alhazan jihar Kebbi zuwa gida Najeriya, ganin cewa sune Alhazan farko da suka fara tashi daga Najeriya zuwa kasa mai tsarki.

Sakataren Hukumar jin daɗin Alhazai na jihar wanda yake kasar Saudiyya tare da shi kansa gwamna Nasir Idris ya jagoranci tawagar wasu jami’an jihar zuwa wasu ofisoshin mahukunta a Makka wanda shirya jigilan Alhazai ya rataya a kansu.

Sakatare Abarshe ya ce ana nan an ci gaba da shirye-shirye domin ganin da an kammal aikin Haji, alhazan Kebbi su cilla zuwa gida.

Jami’an gwamnatin Kebbi da dama da suka zo aikin Hajji suka yi Abarshe rakiya a wannan ziyara da ya yi.

Za a hau Arafat ranar Asabar, wanda daga wannan rana ne za a fara aikin Hajji gadangadan da za a kwashe kwanaki hudu ana yi.

People are also reading