Home Back

Wata Kungiya Ta Shirya Samar Da Gidaje Masu Saukin Kudi 400,000 A Nijeriya

leadership.ng 2024/5/17
Wata Kungiya Ta Shirya Samar Da Gidaje Masu Saukin Kudi 400,000 A Nijeriya

Wata kungiya mai zaman kanta da ke da goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya, mai suna ‘Global Centre For Empowerment And Care For Life Challenges (GECLC)’ ta bayyana cewa, tuni ta kammala shirye-shiryen samar da gidaje masu saukin kudi 400,000 a jihohi 36 na tarayyar kasar nan har da Abuja.

Kungiyar ta ce, wannan na daga cikin kokarinta na cimma muradun karni na Majalisar Dinkin Duniya lamba na 9 da 11 na bukatar samar da gidajen zama kuma masu sauki ga al’umma nan da shekarar 2030.

A jawabinsa yayin kaddamar da shirin a Kaduna, shugaban kungiyar Amb. Bincent Ejikeme Agbo ya ce, a karkashin shirin za a samar da gidaje 10,000 a kowanne jiha a 36 na kasar nan tare da babban birnin tarayyar kasar nan Abuja a matakai biyu da aka tsara.

Ya kuma kara da cewa, a nan gaba za a aiwatar da shirin a wasu kasashen Afrika, amma an kaddamar da shirin daidai da kudurin majalisar dinkin duniya na SDG a Nijeriya ne don ya farfado tare da karfafa shirin gwamantin tarayya na samar da gidaje masu saukin kudi a sassan kasar nan.

Shugaban kungiyar ya kuma ce, “Mun kaddamar da shirin ne don fadakar tare da ilimantar da al’umma a kan muhimancin samar da gidaje masu saukin kudi ga al’umma Afrika kamar yadda dokar muradun karni ta tanada “Sustainable Debelopment Goals (SDG).

“Domin cimma wannan burin mun shirya haduwa tare da tattunawa da dukkan gwamnonin kasar nan da ministan babban birinin tarayya Abuja don fitar da tsarin da za a yi amfani da shi don fara gudanar aikin gina gidajen”.

People are also reading