Rigimar Masarautar Kano: Abba Ya Ba Jami’an Tsaro Sabon Umarni Kan Masu Zanga Zanga
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Kano - Rahoton da muka samu yanzu na nuni da cewa gwamnan Kano, Abba Yusuf ya haramta duk wata zanga-zanga a jihar.
Gwamnan ya kuma ya sanya takunkumi mai tsauri kan duk wani taron jama'a wanda ka iya kai ga yin zanga-zanga a cikin jihar.
Gwamnan ya ba da umarnin ne a wata sanarwa da daraktan yada labaransa, Sanusi Bature ya fitar a shafinsa na Facebook a ranar Laraba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Bisa ga karfin ikon kujerarsa, gwamnan ya umurci ‘yan sanda, jami'an DSS da na NSCDC da su kama, tsare da kuma gurfanar da duk wani mutum ko kungiyar da ke gudanar da zanga-zanga a kan titunan Kano."
- In ji sanarwar Sanusi Bature.
A cewar Bature, gwamnan ya dauki wannan matakin domin dakile duk wani abu da zai iya haifar da karya doka da oda wanda "makiyan jihar ke shiryawa".
“Mun samu sahihan bayanan sirri da ke nuni da cewa wasu fitattun jiga-jigan jam’iyyar adawa a Kano sun tsara shirin daukar nauyin mutane da kungiyoyi domin gudanar da zanga-zanga.
Mun gano za a yi amfani da dalibai da masu fafutukar siyasa daga wasu jihohin Arewa domin tada hargitsi da sunan cewa suna adawa da tsige Sarkin Kano, Aminu Bayero."
Sanusi Bature ya bayyana cewa gwamnatin Kano ta fito karara ta haramta zanga-zanga, ko taron jama'a ko wane iri ne, kuma za a kama wadanda aka samu sun bijirewa umarnin.
Asali: Legit.ng