Dakarun Sojoji Sun Ragargaji 'Yan Ta'adda a Wani Artabu a Jihar Benue
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Benue - Dakarun sojojin Najeriya sun daƙile wani yunƙurin ƴan ta'adda na yin garkuwa da mutane a jihar Benue.
Dakarun sojojin tare da haɗin gwiwar ƴan sa-kai sun ceto wasu mutum biyu da aka so a sace a jihar.
Rundunar sojojin Najeriya ta bayyana hakan a ranar Litinin cikin wata sanarwa a shafinta na manhajar X (wacce a baya aka fi sani da Twitter).
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanarwar ta ce sojojin bayan sun amsa kiran gaggawa, sun kai farmaki a maɓoyar ƴan ta'addan a ƙauyen Tsede da ke kan titin Tor Donga Takum a ƙaramar hukumar Katsina-Ala ta jihar Benue.
Ƴan ta’addan sun ranta ana kare bayan da sojoji suka yi musu luguden wuta, lamarin da ya tilasta musu barin mutanen da suka yi garkuwa da su.
Bayan musayar wutan, an kuɓutar mutum biyu da aka yi yunƙurin sacewa masu suna Cif Sano Kursi da Augustine Sada ba tare da wani rauni ba.
Sanarwar ta ƙara da cewa tuni aka sada mutanen da aka kuɓutar ɗin da ƴan uwansu.
Kayayyakin da aka ƙwato daga hannun ƴan ta’addan sun haɗa da bindiga ƙirar FN guda ɗaya, jigidar bindigar FN guda ɗaya, jigidar bindiga ƙirar AK-47 guda 17.
Sauran sun haɗa harsasai guda 10 na musamman masu kaurin 7.62 mm (Special), harsasai guda 58 masu kaurin mm 7.62 (NATO) da katin ATM 3.
A wani labarin kuma, kun ji cewa dakarun rundunar sojojin saman Najeriya na Operation Hadin Kai da Whirl Punch a Arewa maso Gabas da Arewa ta Tsakiya sun kashe ƴan ta’adda masu yawa a hare-haren da suka kai Borno da Neja.
Jiragen yaƙin sojojin sun kuma lalata gine-gine da kayan aikin da ƴan ta'addan suke amfani da su wajen aikata laifuka.
Asali: Legit.ng