Home Back

Kotu Ta Bayar Da Umarnin Aike Wa Ganduje Da Wasu Sammaci Ta Wasu Hanyoyi Daban

leadership.ng 2024/7/1
“‘Yan Siyasa Ne Aka Bai Wa Gidaje Ba Malaman Makaranta Ba A Kano”

Wata babbar kotu a Jihar Kano, ta bayar da umarnin aike wa shugaban jam’iyyar APC na kasa, Abdullahi Umar Ganduje, da sauran wadanda ake tuhuma a shari’ar cin hanci da rashawa da suke fuskanta sammaci ta wasu hanyoyin na daban.

Gwamnatin Kano na tuhumar Ganduje da mai dakinsa, Hafsat Umar da wasu daga cikin mukarrabansa da zargin aikata laifuffuka 10 masu nasaba da cin hanci da almundahana da karkatar da kudaden al’ummar jihar.

A yayin zaman kotun, lauyan wadanda ake kara, Nureini Jimoh, ya kalubalanci bayyanar da babban lauyan bangaren masu kara, Yau Adamu, ya yi a gaban kotun, inda yace an riga an bai wa wani mutum guda izinin tsayawa bangaren a shari’ar.

Ya’u Adamu ya mayar da martani ta hanyar shaida wa kotun cewar saboda wannan kalubale, Barista Zahraddeen Kofar Mata, ya gabatar da bukatar saurare da yanke hukunci bisa la’akari da uzurin bangare daya na wucin gadi.

Mai Shari’a Amina Adamu-Aliyu ta rushe kalubalantar da Jimoh tare da amincewa da umarnin, biyo bayan bukatar da Kofar-Mata, wanda ke wakiltar bangaren masu gabatar da kara ya yi.

Kazalika, Mai Shari’a Amina Adamu Aliyu, ta umarci bangarorin biyu da ke cikin shari’ar da su gabatarwa kotu izinin bayyana a gaban kotun da suke da shi.

Ta kuma dage zaman kotun zuwa ranar 11 ga watan Yuli, domin ci gaba da sauraron karar.

People are also reading