Home Back

Shugaba Tinubu Ya Yi Allah Wadai da Harin Bam a Borno, Ya Fadi Matakin Dauka

legit.ng 2 days ago
  • Shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu ya yi kakkausar suka kan hare-haren bam da ƴan ta'adda suka kai a ƙaramar hukumar Gwoza a jihar Borno
  • Shugaba Tinubu ya yi Allah wadai da hare-haren waɗanda ya bayyana a matsayin ayyukan ta'addanci
  • Tinubu ya jajantawa waɗanda harin ya ritsa da su, iyalan mutanen da suka rasu da gwamnati da jihar Borno

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Shugaba Bola Tinubu ya yi Allah-wadai da hare-haren bama-bamai da suka haddasa asarar rayuka da raunata wasu mutane da dama a ƙaramar hukumar Gwoza da ke jihar Borno.

Hare-haren na ƙunar baƙin wake sun hallaka aƙalla mutane 18 tare da raunata wasu da dama a ranar Asabar a jihar.

Tinubu ya yi Allah wadai da harin bam a Borno
Shugaba Tinubu ya yi Allah wadai da harin 'yan ta'adda na bam a Borno Hoto: @DOlusegun Asali: Twitter

Me Tinubu ya ce kan harin bam a Borno?

A cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Shugaba Tinubu, Ajuri Ngelale ya fitar a shafinsa na Facebook a ranar Lahadi, shugaban ƙasan ya bayyana hare-haren a matsayin ayyukan ta'addanci.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bayyana cewa harin ya nuna irin matsin lambar da ƴan ta'adda suke sha da kuma nasarar da aka samu na rage ƙarfinsu na kai farmaki.

Shugaban ya bayyana cewa za a hukunta masu tayar da ƙayar bayan domin gwamnatinsa ba za ta bar al’ummar ƙasar nan su shiga cikin wani hali na zaman tsoro da zubar da jini ba.

"Shugaban ƙasa ya bayyana cewa gwamnatinsa na ɗaukar matakan da suka dace domin tabbatar da tsaron ƴan ƙasa, yana mai jaddada cewa za a ƙara himma wajen ganin an kawar da waɗanda ke kawo hargitsi da hallaka rayuka a ƙasa."
"Shugaba Tinubu ya jajantawa waɗanda harin ya ritsa da su, da iyalan waɗanda suka mutu, da kuma gwamnati da al’ummar jihar Borno."

- Ajuri Ngelale

An tayar da bam a Borno

A wani labarin kuma, kun ji cewa an samu asarar rayuka bayan wata ƴar ƙunar baƙin wake ta tayar da bam a garin Gwoza da ke jihar Borno.

Ƴar ƙunar baƙin waken ta tayar da bam ɗin ne a wani wajen taron bikin aure wanda hakan ya yi sandiyyar

Asali: Legit.ng

People are also reading