Home Back

Yanzu-Yanzu: Dalibai 6 Sun Nutse A Kogin Kaduna

leadership.ng 2 days ago
Yanzu-Yanzu: Dalibai 6 Sun Nutse A Kogin Kaduna

Wasu yara ‘yan makaranta su shida sun nutse a jiya Talata, a ƙauyen Ribang, da ke Ƙaramar hukumar Ƙauru ta jihar Kaduna, a lokacin da suke dawowa daga jarrabawar kammala ƙaramar sakandare ta (Junior WAEC).

Waɗanda su ka nutse a kogin Mbang da ke ƙauyen Ribang ɗin sun haɗa da Manasseh Monday da Musa John da Monday Ayuba da Yahuza Audu sai kuma Pius David da David Danlami duk ‘yan tsakanin shekaru 15 zuwa 19 kuma ɗaliban makarantar Sakandaren Gwamnati ne Fadan Chawai.

Jami’in hulɗa da jama’a na ƙungiyar raya Ribang, Fasto Simon Ishaku, wanda ya tabbatar wa manema labarai faruwar lamarin ta wayar tarho a yau Laraba, ya bayyana cewa tuni an gano gawarwaki uku wanda har an binne su, inda ya ce ana ci gaba da neman gawarwakin sauran ɗaliban uku a cikin kogin.

Kogin Mbang ya kasance tarkon mutuwa ga mutanenmu tsawon shekaru, lura da cewa kafin al’umma su samu damar shiga kowace makaranta ko wani asibiti, sai sun yi tafiyar kusan kilomita 8, wanda hakan ya sa al’ummar ke sake kira ga Gwamnati da sauran masu ruwa da tsaƙi na su samar musu da makaranta da Asibiti da hanya da gada domin sauƙaƙa rayuwa.

An tuntubi jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yansandan jihar Kaduna, ASP Mansir Hassan, da ko’odinetan hukumar bayar da agajin gaggawa ta shiyyar Kaduna, Mubarak Muhammad, amma har ya zuwa lokacin haɗa wannan rahoto ba su bayar da wani karin bayani ko wani tabbaci a hukumance ba.

People are also reading