Home Back

Halin ƴan siyasar Najeriya ya fi na sojoji muni - Dalung

bbc.com 2024/7/7

Halin ƴan siyasar Najeriya ya fi na sojoji muni - Dalung

Minti 1 da ta wuce

Tsohon ministan matasa da wasanni, Barista Solomon Dalung ya ce shi a fahimtarsa Najeriya ba ta kai mizanin da ake so ba dangane da romon dimokraɗiyya.

"A shekara 25 ɗin nan a gare ni ba ta haifi ɗa mai do ba....An sami komabaya a tattalin arziki na Najeriya domin a 1999 lokacin da aka kawo wannan dimokraɗiyya, canjin dala a lokacin yana ƙasa da naira 10 amma a yau muna maganar kusan naira 1500." In ji tsohon ministan.

Dangane da ilimi, Dalung ya ce "ba ma za ka taba haɗa ingancin ilimi na wancan lokacin da na yanzu ba."

Harkar noma da kiwo da zamantakewa da tsohon ministan ya yi magana a kai, ya ce duka komabaya aka samu.

Da aka tambaye shi ko daga wane lokaci al'amura suka taɓarɓare kasancewar shi ma ya kasance a wata gwamnati a baya. Sai ya ce " tsarin ne ba mai kyau ba. Idan da a ce irin na Birtaniya ne da shugaban ƙasa dole sai ya yi shawara da majalisa kafin yanke hukunci. Amma yau shugaban ƙasa zai yi gaban kansa ya bai wa hukumar alhazai kaza, wannan kaza."

Halin 'yan siyasa ya fi na sojoji muni

Solomon Dalung ya ce abin takaici shi ne yadda halayen ƴan siyasa ya yi muni fiye da na sojoji.

"Abin da 'yan siyasa suke yi ya fi na sojoji muni a yanzu bisa rashin tausayin da suke nunawa da kuma halin matsi da suka jefa 'yan Najeriya."

Sai dai kuma ya ce sojojin ne suka lalata al'amarin mulkin dimokraɗiyya a Najeriya.

"Sojoji sun azabtar da 'yan siyasa sakamakon fadi tashin da burgimarka hankaka da suka yi."

Daga ƙarshe barista Dalung ya ce abin da ke tayar masa da hankali shi ne irin halin matsin da ƴan Najeriya ke ciki a yanzu.

Me Dalung ya cimma a matsayin minista?

"Sai da kudi ake aiki. Ai komai iya dabo sai da laya. Ki je ki duba kasafin kudin kasar nan na 2016, majalisa ba ta ware min ko kwabo ba domin gudanar da ayyuka." In ji Dalung.

Sai dai kuma tsohon ministan ya ce manyan ayyukan da ma'aikatarsa ta yi shi ne "na bi shugaban ƙasa da kungiyoyi masu zamna kansu waɗanda suka bayar da gudunmowa na kuma gudanar da wasu abubuwan da suka taimaka. Amma kin san tsari irin na majalisar gwamnatin tarayya ita ce wadda a ƙarshe za a fahimci ci gabanta."

People are also reading